Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa za ta shirya wata bita ta musamman domin wayar da kan ma’aikatan ta na sashen fadakar da masu zabe da ke hedikwatar ta da kuma jihohi.
Wata sanarwa da ta fito daga hukumar a ranar Asabar ta ce bitar, mai taken “Fadakar da Mai Fadakarwa”, wato “Train-the-Trainers, an kasa ta zuwa gida biyu saboda matsalar annobar korona (COVID-19) da ake fama da ita.
Kashin farko za a yi bitar ga shugabannin sashen fadakar da masu zabe (HODs VEP) da ke jihohin Kudu da kuma wadanda su ke a hedikwata a Abuja. Za a yi nasu daga ranar 1 zuwa ranar 3 ga Maris, 2021 a otal fin ‘Royal Bird Hotel’ da ke unguwar Alagbaka, GRA, Akure, Jihar Ondo.
Kashi na biyu na bitar za a yi wa shugabannin sashen fadakar da masu zaze (HODs VEP) da ke jihohin Arewa da na hedikwata da ke Abuja daga ranar 11 zuwa ranar 13 ga Maris, 2021 a garin Lokoja, Jihar Kogi, amma ba a tsaida wurin da za a yi ta ba.
Haka kuma wannan bita, wadda za a shirya ta ne tare da hadin gwiwar Gidauniyar Tsare-tsaren Zabe ta Duniya (International Foundation for Electoral Systems, IFES), za ta amince da Kundin Wayar da Kan Masu Zabe wanda jami’an Hukumar Zaɓe da ke hedikwata su ka riga su ka kammala duba shi.
Bugu da kari, bitar za ta bada dama a bayyana wa shugabannin sashen fadakarwar ayyukan da hukumar ta sanya a gaba da su ka hada da: fadada hanyar da masu zabe za su samu isa ga rumfunan zabe; da aikin cigaba da yi wa masu zabe rajista wanda ke tafe; da Babban Shirin 2022-26; da batun zaben gwamnan Jihar Anambra; da kuma yin musayar ra’ayi kan abubuwan da su ka gudana a lokacin Babban Zaben da aka yi a shekarar 2019.