Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta bayyana irin aikin da ya rataya a wuyan ta wajen aikin gyaran iyakokin mazabun da ke kasar nan.
Babban Kwamishinan Kwamitin Yaba Labarai da Wayar da kan Jama’a na hukumar, Mista Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.
Okoye ya ce hukumar ta lura da wasu rahotanni da ke yawo a kafafen yada labarai daban-daban a kan hakkokin hukumar wajen rarrabawa, sake nazari da kuma gyara kan iyakokin mazabu a Nijeriya.
Ya ce ganin haka ne ya sa tilas hukumar ta ga ya kamata ta fito ta bayyana matsayin ta a bisa tsarin mulki a wannan aikin.
Ya ce, “Saboda a tabbatar da fahimtar jama’a kan al’amarin, hukumar na so ta yi bayanin abin da tsarin mulki ya dora mata da kuma abin da ta ke yi a kan hakan.
“Da yake karkasa kasar nan zuwa zuwa mazabun Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai da Majalisun Jihohi haƙƙin hukumar ne, da zaran an fitar da su, sauran aikin sake nazarin mazabun tare da ko yi masu kwaskwarima aikin hadaka ne na ita hukumar da Majalisar Tarayya.
“Saboda haka, duk wani sake tsari ko gyara irin wannan ba zai yiwu ba sai bangarorin nan biyu na Majalisar Tarayya sun amince da shi, wato Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai.”
Okoye ya bayyana cewa a dalilin wannan muhawarar, hukumar ta na zantawa da kwamitocin Majalisar Tarayya da su ka dace domin a shirya zama da shugabannin majalisar saboda a tunkari wasu daga cikin manyan matsalolin rarrabawa da sake nazari da kuma gyaran mazabun a Nijeriya.
A cewar sa, wasu daga cikin matsalolin, wadanda a baya hukumar ta nuna wa Majalisar Tarayya su, sun hada da wadannan:
“Tsarin Mulki na 1999 (a yadda aka yi masa kwaskwarima) bai dora wa INEC alhakin sake nazari ko sauya kan iyakokin mazabu ba bayan kowane shekara 10, kamar yadda aka faɗa a wasu ra’ayoyi a kafafen yada labarai. Don cire duk wani shakku, Sashe na 73 (1) na Tsarin Mulki ya tanadi cewa aikin zai rika faruwa jefi-jefi ‘mafi karancin shekara 10’.”
“Hakan ya nuna cewa za a iya yin hakan ne kadai daga shekara 10 zuwa sama. Don haka, hukumar ba ta saba wa Tsarin Mulki ba, tunda dai za a iya sake nazarin ne a cikin shekara 10 kadai zuwa sama.
“Haka kuma Tsarin Mulki ya tanadi cewar hukumar za ta iya fara aikin sake nazarin da yin gyaran idan an gudanar da aikin kidayar jama’a ta kasa, kirkiro jihohi ko idan Majalisar Tarayya ta zartar da Doka [Sashe na 73 (2)]. A yanzu babu ko ɗaya daga cikin wadannan abubuwan da su ka faru.
“Aikin kidayar jama’a na karshe da aka yi an yi shi ne a cikin 2006, kimanin shekara goma sha biyar kenan.
“Hukumar ta na ganin cewa sake nazari ko tare da sake tsarin mazaɓun bisa bayanan shekara 15 da aka tattara bai dace ba saboda kowa ya san saurin ƙarin yawan jama’a da ake samu a Nijeriya zai sa a ga shirme a duk wani sakamako da aka samu.
“Ko ma dai yaya ne, Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa ta na nan ta na kokarin sake wani aikin kidayar kuma akwai alamar dacewar a jira a ga sakamakon shi.
“Ta wani bangaren, ba a kirkiro wasu sababbin jihohi ba a Nijeriya tun daga lokacin da aka yi Tsarin Mulki a cikin 1999 sannan babu wata Dokar Majalisar Tarayya da aka yi mai bukatar INEC ta fara aiki da wasu sassan Tsarin Mulki da su ka dace da batun karkasawa, sake nazari ko sake tsarin mazaɓun zabe.”
Kwamishinan hukumar zaen ya kara da cewa a kan batun mazabun jihohi da za a kirkira a kowace jiha ta tarayyar kasar nan, Tsarin Mulki ya tanadi cewa yawan wadanda za a yi a kowace jiha ya kasance ninki sau uku ko sau hudun yawan mazabun tarayya (kujerun Majalisar Wakilai), ya danganta da mafi ƙarancin 24 da kuma mafi yawan 40.