Ina jinjina wa salon wakilcin Uba Sani a Majalisar Dattawa – El-Rufai

0

Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya jinjina wa salon wakilcin Sanata Uba Sani a Majalisar Dattawa da Honarabul Garba Datti a Majalisar wakilai bisa kyawawan wakilci da suke yi wa jihar Kaduna a Majalisun tarayya.

El-Rufai cikin annashuwa, farinciki da bugun kirji ya bayyana sanata Uba Sani a matsayin nagartaccen wakili mai kishin talakawa, Jama’an jihar Kaduna da Najeriya baki daya.

El-Rufai ya bayyana wasu kudirori hudu da sanata Uba Sani ya dauki nauyin su a majalisar dattawa da ya hada da baiwa jihohi karfin iko akan jami’an tsaro maimakon yadda yake a dunkule sai gwamnatin Tarayya ta ba da izini a matsayin abin alfahari da kuma abin a yaba.

Idan ba a manta ba gwamnatocin jihohi ko na kananan hukumomi ba su da iko akan jami’an tsaro dole sai an ba su umarni daga Abuja ko mai gaggawar abin.

Dalilin haka ne ya sa Sanata Uba Sani ya ga cewa abinda ya fi dace wa shine a baiwa jihohi wannan iko na iya ba jami’an tsaro umarni a duk lokacin da hakan ya taso ta hanyar yin doka da zai ba su damar haka. Wato ace ko wacce jiha ko karamar hukuma gwamna ko shugaban karamar hukuma yana da ikon da zai umarci jami’an tsaro cikin gaggawa akawo karshen rashin wani tashin hankali.

Sau da dama jira sai jami’an tsaro na ‘yan sanda ko sojoji sun jira umarni daga Abuja kafin su iya afkawa wani tarzoma ko tashin hankali komai tsananin sa, hakan na sa a rasa rayuka da dukiyoyi da dama.

Wannan kudiri idan har ta zama doka zai warware wannan kulli ya ba jihohi da kananan hukumomi damar amfani da jami’an tsaro a jihohin su yadda ya kamata da kawo karshe rashin tsaro cikin kankanin lokaci.

Share.

game da Author