Hisbah ta kama mota dankare da jarkoki da kwalaben giya a Kazaure

0

Hukumar Hisbah a jihar Jigawa ta kama mota dankare da jarkoki da kwalaben giya a karamar hukumar Kazaure.

Kwamandan Hisbah, Dahiru Garki, ya shaida wa Jaridar PREMIUM TIMES HAUSA, cewa hukumar tayi kama jarka har 25 cike makil da giya a wata mota kirar Tayota Corona da kuma kwalabe na giya 364.

Ustaz Dahiru, yace an kama motar ne a ranar 17 Maris da misalin karfe 9 na safe bayan samun bayanan sirri dangane ga jigilar kayan giyar a karamar hukumar ta Kazaure.

A baya hukumar Hisbah ta farfasa kwalaben giya har kimanin 2,875 da kuma jarka hudu na Burkutu a samame da ta kai wasu wurare da dama da ake kwankwadar giya a fadin Jihar, inji Dahiru.

Kwamandan yace sai da kotu ta bada umarni kafin hukumar Hisbah ta aiwatar da farfashe kwalaben giyan da ta kwace.

Shugaban ya jaddada cewa shan Giya, da Siyar da ita da kuma safarar ta, laifi ne a Jihar Jigawa, saboda haka hukumar bazata yi kasa a guiwa ba wajen yaki da ta’ammali da Giya da sauran laifuffuka irin haka a Jihar.

Dahiru ya kuma yi kira ga al’ummar Jihar dasu bada gudunmawarsu wajen yaki da laifuffuka ta hanyar bada bayanan sirri ga hukumar Hisbah domin samun nasara.

“A musulunci, kama laifi aikin al’ummane ba sai jami’in tsoro ba kadai, ya zama wajibi ga AI’umma su bada tasu gudunmawar wajen wamzuwar tarbiya nagari bisa tsarin musulunci” Dahiru

Share.

game da Author