HIMMA DAI MATA MANOMA: Rangadi A Gonar Ebimoboere: Matar Da Ta Yi Wa Maza Zarra Wajen Noma Kayan Miya Mai Yawa

0

Ebimoboere Eniyekpemi mace ce mai shekaru 28 kadai a duniya. Amma tun a yanzu ta yi fice, ta yi zarra kuma ta zama gagarabadau a bangaren noman kayan miya a Jihar Delta. Idan ka yi wa Ebimoboere kirarin cewa, ‘macen da ta fi namiji 100 himmar noman kayan miya’, to a gaskiya ta cancanci wannan kirarin, domin kusan hakan ta ke.

Mutum ba zai tabbatar ba, har sai ya shiga gonakin ta ko manyan lambunan ta, a jihar da ake wa kallon kamar ba zai yiwu a shugaba irin su albasa, tumatir, gurji da su alayayyahu su yi albarka ba, to ita dai a yanzu ne ma ta ke cin gajiyar albarkar kayan noman da ta ke shukawa masu tarin yawa.

Ta shiga harkar noma bayan ta kammala digiri na farko a fannin kimiyyar ilmin tsirrai da shuke-shuke, a yanzu kuwa a harkar noma ta na a sahun gaba. Ita ce mai kamfanin Afritropic Farming anda Agro Services Ltd (AFAS).

Wannan mata ba noma kadai ta ke yi a maka-makan gonakin ta biyu a jihar Delta ba. Ta na sayar da kayan noma na zamani, kuma kamfanin ta na horas da sababbin-shigar wata harkar noma dabarun noman.

A yanzu haka akwai ma’aikata har 42 a kamfanin ta, sannan kuma akwai ma’aikatan wucin-gadi 113 duk masu cin moriyar aiki a karkashin ta.

Wannan matashiyar mata ko auren fari ma ba ta taba yi ba. Ta bayyana wa wakilin mu cewa ta shiga harkar noma a cikin 2014.

Ta yi sha’awar fara jaraba noma, ganin cewa ana samun karancin kayan miyar da ake kaiwa jihar Delta daga Arewa.

Ta ce ta na mamakin da ake cewa wai ko an shuga irin su Timatir, albasa, alayyahu, gurj da sauran su, to ba za su yi ba a can saboda kasar Delta ba za ta yi wa wadannan kayan ba.

Dalili kenan ta ce ita kuwa tunda ta na da kwarewa da gogewar horon sanin dabarun shuke-shuke tun a jami’a.

Sai dai kuma ta ce akwai kalubalen da ta ke fuskanta. “Akwai wasu kayan aikin noma wadanda mutum da kudin sa ma wuyar samu su ke yi. duk da haka ta ce amma ita ta na kallon kan ta a matsayin mai yin noman sayarwa, mai noma kayan gonar da za a iya tasawa a gaba ba ana ci.

“Ni ba na fuskantar irin kalubalen da kananan manoma ke fuskanta a Jihar Delta, saboda ina yin noma mai yawa.

“Kuma mu na kokarin ganin mun cike gibin da kananan manoma ke shan wahala.

“Amma kawai abin da zan iya cewa dangane da kalubalen manoma ko kananan manoma a yankin Neja-Delta, ita ce matsalar karanci da rashin wadatar gonaki, ko filayen noma.

“Akwai daji sosai, amma fa surkukin jeji ne. Samar da da katafilar da za a yi aikin da za a sassabe wannan surkukin daji ba karamin jidali ba ne.

“Abu na biyu kuma shi ne noman rani, wato ban-ruwa. Kamar ni ina kashe naira 800,000 zuwa 900,000 kafin a gina min rijiyar burtsatse daya tal.

“To ka ga kenan karamin manomi ba zai iya gina rijiyar burtsare ko guda daya ba.

“Sannan kuma ka ga noman rani, kayan gona ne wadanda ba su son ana ajiye su tsawon lokaci, sai su lalace.

“To rashin kayan ajiya ko adana amfanin gonar shi ma babbar matsala ce.

“Idan kuma ka ajiye su wurin da bai dace a ajiye su ba, to lalacewa za ka yi, ko su rube ko su nukake. Musamman alayyahu da tumatir da sauran su.”

A halin yanzu wannan mata ta yi hadin guiwa da Gwamnatin Jihar Delta, inda ta ke horar da matasa masu tarin yawa, a karkashin shirin AAGDS.

Batun yawa ko fadin gonar ta kuwa, ta bayyana cewa akwai mai mai fadin hekta 50 wadda ta karba aro daga hannun gwamatin jiha, sannan kuma akwai mai fadin hekta 60, wadda ya saya da kudin ta.

An taba gayyatar da Amurka, inda ta je ta yi kwas da horon sanin makamar aikin gona.

“A nan manomi na shan wahala kafin ya samu kayan aikin noma na zamani. Amma a Amurka, sai ka ga akaya na naira milyan 20 daya tal an damka wa manomi lamuni.”

Ta bayyana wa wakilin mu cewa ta na cikin kungiyar manoma matan da su ne su ka kafa ta. Kuma ta ce ita dai da ya ke ta na da karfi a fannin noma, to babu wani bambancin jinsin da maza ke mata idan batun cin moroyar wani hasafi ne daga gwamnati.

Share.

game da Author