Nike mace ce mai himmar noma, wadda ta kama sana’ar noma gadan-gadan cikin cikin 2017, a jihar Osun.
Shawararfarko da aka bata kafin ta fara, ce mata aka yi ta fara kiwon kaji guda 100.
Kafin ta shiga harkar kiwon kaji, Nike ta kammala digiri na farko kan Tarihi da Nazarin Huldar Diflomasiyya. Sai dai kuma dan abin da ta ke samu ne ta ga bai ishe ta biyan bukatun yau da kullum ba.
Ana biyan ta bakin gwargwado, sai dai kuma duk da haka, sai ta yi shawarar ajiye aiki cikin 2016, ta shiga harkokin kiwon kaji.
Abu kamar wasa sai ga shi Nike ta samu nasibin kiwon kaji, ta yadda harkar ta bunkasa, yanzu ita ce shugaba ko Manajar Daraktan Azarel Farms.
“Ni dama tun tuni ina sha’awar harkokin noma da kiwo. Ina wasu harkokin amma dai a yanzu na fi bada karfi a harkokin noma da kiwo.” Haka ta shaida wa PREMIUM TIMES.
Wani masanin dabarun kiwon dabbobi ne ta tuntubi shawara, shi kuma ya ce ta fara da jaraba kiwon kaji 100.
Da farko rainawa ta yi, amma zuwa cikin 2018 sai gas hi garken kajin ta sun kai 500.
Nike matar aure ce, mai yara uku, kuma yanzu haka mamba ce Kungiyar Masu Kiwon Kaji, rashen jihar Osun.
Ta shaida cewa shiga wannan kungiya ana damawa da ita ya kara mata nasibi a fannin kiwon kaji.
Sannan kuma Nike ta na da difiloma a fannin shari’a, amma duk ta ajiye a gefe guda, ta fadada wata gona ta ke kiwon zomaye da kayan ganyayen miya. Ta ce ta na kiwon zomaye sun kai 120.
Saboda ta san daraja da muhimmancin ilmi, Nike ta rika amfani da wannan dama ta na zuwa koyon horon dabarun kiwo ko na noma.
Shigar ta cikin Kungiyar Masu Kiwon Kaji ta Jihar Osun, ya karfafa kungiyar a cikin 2018, inda mambobin ta su ka samu tallafin kudade daga gwamnatin jihar Osun.
Tallafin da ta samu shi ne kudaden sayen ‘yan tsakin sabuwar kyankyasa har 2,000, sai kuma abincin kaji, magungunan su, allurai da kuma wadansu abubuwa da ake bukata domin harkokin kiwon kaji su tafi ba tare da wata tangarda ba.
Wannan tallafi ya bunkasa masu harkokin kiwo,ta yadda duk bayan makonni 7 ta na sayar da kaji masu tarin yawan gaske.
PREMIUM TIMES ta shiga har cikin gonar Nike mai fadin hekta hudu. Yanzu kuma ta kara fadada gonar.
A gonar ta ake yanka kajin kuma a rika sayarwa. Ta ce abin ya na yi mata ciwo idan ta ga matashi ya na ta gaganiyar neman aiki, alhalin ga sana’ar noma a kofar gidan sa, ya rufe ido, shi kuma bai sani ba.
“Abin ya na kona min zuciya, idan nag a matashi sai wahalar neman aiki ya ke yi, alhalin ga noma nan, bai maida hankali a kan sa ba.
“Ko kiwon zomaye matashi ya kama, to cikin kankanin lokaci zai samu zomaye masu yawa.” Inji ta.
“Ana saida auren zomo naira 2500. Idan ka sayi aure hudu kan naira 10,000, to cikin wata uku garken zomayen ka zai habbaka. Kuma za ka iya sayar da tsoffin zomayen sama da naira 5000.’’ Inji Nike.
Discussion about this post