Kayode Fayemi ya shaida cewa wasu ‘yan kakuduba aka turo musamman su ka ce za a ba shi dala milian 80 idan ya amince aka biya su kudaden.
Gwamna Kayode Fayemi na Jihar Ekiti, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, ya bayyana a ranar Litinin cewa wasu ‘yan gidoga sun same shi gaba da gaba, su ka yi masa alkawarin cewa idan ya amince aka biya bashin da kotu tace a biya su na dala miliyan 418, to za su ba shi cin hanci har na naira bliyan 80.
Bashin dai wanda ake tankiya a kai, masu neman a biya su bashin sun yi ikirarin cewa jihohi da kananan hukumomi ne ake bi bashin a daidai lokacin da ake karin karbo kudade da ga Paris Club.
Sun ce sun yi wa jihohi da kananan hukumomin kasar nan 744 ayyuka ne bashi, bisa yarjejeniyar cewa idan aka biya jihohi da kananan hukumomi kudaden Paris Club, to za su biya su.
A cikin wata tattaunawa ta musamman da Gwamna Fayemi ya yi da PREMIUM TMES, ya bayyana cewa da farko alkawarin ba shi dala miliyan 40 su ka yi. Ya ce ba ya bukata, kuma ba zai bari a biya su kudaden ba, tunda babu wata hujjar da ke nuna cewa sun yi ayyukan da su ke ikirarin sun yi.
Fayemi ya ce sun sake samun sa, su ka yi masa alkawarin biyan sa toshiyar baki ta dala miliyan 80, wato nunkin dala milyan 40 kenan. A nan ma gwamnan ya ce ba ya bukata, ba zai karba ba.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin yadda kakudubar ta ke da kuma yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami, Ministar Harkokin Kudade Zainab Ahmed da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari su ka rika kokarin su ga an biya ‘yan kakuduba kudaden, duk kuwa da cewa Kungiyar Gwamnanonin Najeriya sun kai wa Shugaba muhammadu Buhari takardar cewa kada biya kudaden, har sai an yi kawakwaran binciken kwakwaf an tabbatar tukunna.
Baya ga gwamnnin, Hukumar EFCC da Kungiyar ALGON ta shugabannin kananan hukumomin Najeriya, ita ma ta yi kashedin kada a biya kudaden, duk ga Minista Malami, amma ministan ya kauda kai daga gargadin su, ya ci gaba da kokarin ganin sai an biya kudaden daga kudaden jhohi da kananan hukumomi.
“Wato maganar gaskiya mamaki ya kama ni ganin yadda wadanda aka turo mn ko kunya ba su ji ba, su ka tunkare ni da batun ba ni cin hanci har na dala milyan 40. Daga nan su ka nunka farashi zuwa dala milian 80.” Inji Fayemi.
Fayemi a ce shi bai kullaci wadanda su ka yi ikirarin su na bin bashin ba. Kuma bai ce ba ya so a biya su ba, amma abin da ya jajirce a kai a matsayin sa na Shugaban Kungiyar Gwamnnin Najeriya, shi ne kafin a bia kudaden, a fara gudanar da binciken kwakwaf domin a gano shin sun yi ayyukan ko kuwa ba su yi ba.
Ya kara da cewa maganar neman a biya shi cin hanci na dala har miliyan 80, hakan na kara tabbatar da cewa akwai lauje a cikin nadi.