Wani tsohon farfesa Mai shekaru 80 mai suna Muritala Haroon, ya kai kukan sa kotun gargajiya dake Mapo domin ta kwato masa hakkin sa cewa matarsa Afsat bata yadda ya kusanceta a duk lokacin da ya matsu.
Haroon ya kai kara da ranar Alhamis inda yake neman kotun ta raba auren sa da Afsat wanda auren yakai tsawon shekaru 52 suna tare.
Ya ce Afsat taki bin umarnin Kotu a zamanta na farko inda tace lalli ta rika barin shi ya na ida bukatarsa idan hakan ya taso, amma taki.
Sai dai kuma a wannan zama wato karo na biyu, Afsat bat zo ba kuma bata aiko da wakili ba.
Alkalin kotun Ademola Odunade ya roki Haroon ya kara hakuri cewa kotun za ta tattauna da magabatan su domin kawo karshe wannan matsala.
Za a ci gaba da Shari’a ranan 17 ga Mayu.
Idan ba a manta ba a watan Fabrairu ne farfesa Haroon ya shigar da kara a karon farko inda yake neman a raba aurensa da Afsat matarsa.
Haroon ya ce matarsa na yawan koransa daga dakinsu na kwana sannan ta hada baki da ‘yan uwanta su kashe shi.
Ya ce a halin da ake ciki Afsat ta karkatar da hankalin ‘ya’yan su shida domin su juya misa baya a gida. sam basu daraji a matsayin sa na mahaifin su.
Sai dai tun a lokacin, ita Afsat ta roki Kotu kada ta raba auren, ta ce a barsu su ci gaba da zama haka nan. Ta koka a gaban kotu cewa shi farfesa Haroon, yana bibiyan matan mutane. Harda matan mutumin dake sasantasu idan suka samu sabani a tsakanin su.