HANA SHAWAGIN JIRAGE A SAMANIYAR ZAMFARA: Mu zuba mu gani ko hakan zai kawo karshen ‘yan bindiga a jihar – Matawalle ya ja daga da Buhari

0

Idan ba a manta ba bayan kammala taron Kwamitin tsaro da aka yi a fadar shugaban Kasa ranar Talata, shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya saka tsauraran dokoki a jihar Zamfara domin fatattakar ‘Yan bindiga da ke sheke ayarsu a jihar da yankin Arewa maso Yammacin kasar nan.

Mai baiwa shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaron Kasa, Babagana Monguno ne ya bayyana matsayar gwamnati a zantawa da yayw da manema labarai bayan taron.

” Daga yanzu ba a yardarwa wani jirgi yayi shawage ko ya ratsa ta sararin samaniyar jihar Zamfara ba, sannan kuma gwamnati ta hana ayyukan hako ma’adinai da ake yi a jihar.

Buhari ya ce ” Ba za mu zuba ido, ana yi mana yadda aka so ba domin bata mana suna ta hanyar ayyukan hare-haren yan bindiga a kasar nan ba. Tura fa ta kai bango yanzu. Duk wanda ake zargi da hannu ko kuma ingiza tada zaune tsaye zai kuka da kansa.

” Duk wanda yake ganin shi shafaffe da mai ne zai rika ruruta wutar tada hankalin jama’a da hada wata alaka da ‘yan bindiga, dubun shi ya cika shi da’ yan bindigan yanzu zai.

Martanin Matawalle

A ziyarar jaje da gwamnan jihar Ekiti ya kai wa gwamna Matawalle Gusau, Gwamnan ya soki wannan matsaya ta gwamnati wato na hana shawagin jiragen sama a sararin samaniyar jihar zamfara saboda samar da tsaro da kuma ba sojoji daman iya gamawa da ‘yan bindiga.

” Wannan matsaya na gwamnatin Tarayya bai yi min dadi ba kwata-kwata amma tunda sunce haka suke so bari mu zuba mu gani za hakan zai haifar musu da da mai ido ko kuma kunya ce za su sha a idanun ‘yan Najeriya.

” Nima fa gadon wannan tsahin hankali na yi daga gwamnatin baya.

” Yan Najeriya sun zura ido su gani ko matsayar da gwamnati za ta dauka zai iya kawo karshen ‘yan bindiga. Amma wannan shawara da su ka dauka, za su gani a kwanon cin tuwon su ko hakan zai kawo karshe ‘yan bindiga ko kuma ‘yan Najeriya za su gane ‘ashe shayi kawai su Buhari’ da makarraban sa suke sha a irin wannan ganawa.

Jaridar Daily Trust wacce ta ruwaito labarin ta bayyana cewa, a karshe gwamna Fayemi ya yi kira ga gwamnan da gwamnatin tarayya su zauna a teburin shawara domin a samu matsaya daya don ci gaban Najeriya.

Share.

game da Author