Hana jirage ratsa sararin samaniyar jihar Zamfara zai taimaka wajen kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga -In ji Ganduje

0

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje ya bayyana cewa ya yi na’am da umarnin shugaban kasa na kada jirage su rika ratsa sararin samaniyar jihar Zamfara daga yanzu.

Ganduje ya ce yin haka zai kawo karshe hare-haren ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

” Maimakon a maida abin siyasa, a yi masa kyakkyawar zato. Bayannan sirri na tsaro ne ya gano cewa akwai masu amfani da jirage masu saukar angulu suna sauka da tashi a dazukan Zamfara. Wanda sune suke yi wa mahara jigilar abinci da makamai.

” Sannan kuma idan ba a manta akwai arzikin kasa na gwal a wannan yanki, ana fakewa da aikin hako ma’adinai a ana tafka aika-aika a dajin.

Ganduje ya ce maimakon a maida abin siyasa, a bari tukunna a ga irin dan da wannan tsari zai haifar tukunna.

Share.

game da Author