Gwamnatin Tarayya na bukatar fili mai hekta 100,000 domin noman shinkafa a Jihar Nassarawa

0

Gwamnatin Tarayya ta bukaci jihar Nasarawa ta nuna mata fili mai cin hekta 100,000, inda za ta bunkasa noman shinkafa a jihar.

Gwamnan Jihar Nasarawa Abdullahi Sule ne ya bayyana haka a ranar Talata, lokacin da ya karbi bakuncin tawagar Hukumar Raya Kogin Benuwai, wadda Manajan Daraktan Hukumar Muhammad Addra ya jagoranta.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta yi alkawarin cewa ita za ta bayar da kudaden aikin noman har ma da bayar da irin shinkafar da za a noma, ga dukkan manoman da za su ci moriyar noman shinkafar a jihar Nasarawa.

“Jiya-jiyan nan su ka kira ni daga Abuja, su ka shaida min cewa su na cigiyar tangamemen filin da zai kai fadin hekta 100,000 wanda gwamnatin tarayya za ta rika samar da kudaden da za a bunkasa noman shinkafa a nan Jihar Nasarawa.” Inji Gwamna Sule.

“Idan aka samu filin, gwamnatin tarayya ce za ta katse filin, ta sassabe shi, ta bayar da kudin aiki sannan ta bai wa manoman irin shinkafar da za a shuka.”

Shinkafa na daya daga cikin abincin da aka fi ci a Najeriya. Wata kididdigar da Hukumar Bunkasa Harkokin Noma ta Amurka ta gudanar cikin 2020, ta ce an noma akalla 5040,000 metrik ton na shinkafa, amma shinkafar da aka ci a kashekar ta kai metric ton 6700,000.

Gwamna Sule ya ce Hukumar Bunkasa Noman Rani ta Koin Benuwai ta na da shimfidaddiyar kasar filin noman shinkafa har fulotai 200,000 a Tide.

Don haka gwamnatin Nasarawa za ta sadaukar wa gwamnatin tarayya wani bangare na wannan shimfideden fili domin noman shinkafar da ake bukata.

Karshe ya ce gwamantin sa za ta ci gaba da bayar da goyon baya ga Hukumar Bunkasa Noman Rani ta Kogin Benuwai.

“Zan ci gaba da bai wa hukumar ku goyon baya wajen bunkasa harkokin noman rani a jihar nan. Musamman ma ga shi yanzu Jihar Nasarawa ta ware fili hekta 500 domin bai wa matasa su yi noman shinkafa a Madatsar Ruwan Doma.”

Share.

game da Author