Gwamnan Ondo ya biya wa dalibai 25,736 kudin jarabawar WAEC ta shekarar 2021

0

Gwamna Oluwarotimi na Jihar Ondo ya amince a biya iyayen dalibai kudaden jarabawar WAEC da su ka rigaya su ka biya wa ’ya’yan su.

Daliban dai wadanda za a maida wa kowa kudin jarabawar da aka biya masa, su 25,736 ne. Sun rigaya sun biya kudaden domin rubuta jarabawar WAEC ta shekarar 2021.

Babban Sakatare ta Ma’aikatar Ilmi, Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ondo, Lola Amuda ce ta bayar da wannan umarnin ga dukkan shugabannin makarantun sakandare gwamnatin jihar, a ranar Laraba.

Ta bayar da wannan sanarwa ce a Akure, babban birnin Jihar Ondo, a lokacin da ta ke jawabi wurin taro da Kungiyar Dukkan Shugabannin Makarantun Sakandare (ANCOPSS) da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin inganta ilmin jihar.

Kudaden wadanda Gwamna Akeredolu ya amince zai mayar wa iyayen dalibai sun kai naira miliyan 360, wadanda dalibai 25,736 su ka biya.

Wannan tsari a cewar gwamnatin jihar, ya yi daidai da shirin da gwamnatin Ondo ke yi na bayar da ilmi kyauta.

Lola gargadi shugabannin makarantun sakandaren su taya gwamnatin jihar ganin cewa daliban sun yi matukar kokari da bajinta sosai wurin jarabawar da su yi ta WEAC din.

Ta ce shugabannin makarantu su ne idanu kuma su ne kunnuwan gwamnati a ckin makarantu.

Don haka ta kara yin kira a gare su cewa su rika aiki da tsare-tsaren da gwamnatin Ondo ke bijirowa da su a makarantun su.

Share.

game da Author