Gwamnan Obaseki zai yi allurar rigakafin Korona a bainar jama’a kowa ya shaida yayi

0

Idan ba a manta ba a ranar Alhamis ne sakataren gwamnatin jihar Edo Osarodion Ogie ya bayyana cewa gwamnati ta karbi kwalaben maganin rigakafin cutar korona na ‘AstraZeneca’ daga gwamnatin tarayya.

Ogie yace gwamnati ta tsara hanyoyi da za a bi wajen ganin an yi wa mutanen jihar rigakafin jihar ba tare da an samu matsala ba.

Sai dai Sakataren gwamnatin bai fadi adadin yawan kwalaben maganin rigakafin da gwamnati ta karbo ba.

Gwamnan jihar Godwin Obaseki ya bayyana cewa shi ne za a fara yi wa allurar rigakafin cutar Korona kuma za a yi ne a bainar jama’a domin kowa ya shaida yayi rigakafin.

Obaseki ya ce yin haka zai taimaka wajen kara wa mutane karfin guiwa wajen amincewa a yi musu allurar rigakafin.

A ranar Talata ne rigakafin Korona miliyan 4 suka iso kasar nan.

Da ma kuma tun a safiyar Talata, Mustapha ya shaida cewa Najeriya na da wuraren da za a jiye maganin ana yi wa mutane.

Sannan kuma ya kara da cewa gwamnati za ta saka ido domin kada a yi harkallar maganin wanda shine yanzu kwamitin za ta fi maida hankali a kai.

Ya ce za a saka jami’an tsaro, EFCC, ICPC da sauransu domin taya kwamitin sa ido kada a aikata ba daidai ba da maganin.

Share.

game da Author