Kamfanin sadarwa na MTN ya yi ciniki da kuma samun ribar da bait aba yi ba a Najeriya, har na naira tiriliyan 1.346 a cikin shekarar 2020.
MTN ya samu wannan gagarimin ciniki ta hanyar samun kudin shiga dalilin sayen data da aka rika yi a lokacin zaman korona, har ta naira bilyan 332.413.
Wannan ciniki da MTN ya samu a cikin 2020, ya kai shi ga zama kamfanin da ya fi kowane kamfani samun kudi a Najeriya, kasar da ta fi sauran kasashen Afrika karfin tatalin arzki, a cikin shekarar 2020, shekarar da korona ta kuntata wa tattalin arzikin kasashen duniya baki daya.
A Najeriya dai Masana’antar Siminti ta Dangote Cement Plc ce kadai ta fi MTN karfin jari da karfin arziki. Wato MTN ke na biyu kenan.
MTN ya samu karin kudin shiga a 2020 da kashi 15 bisa 100, wato daga naira tiriliyan 1.70 cikin 2019, zuwa cinikin naira tiriliyan 1.346 cikin 2020.
Cinikin ya samu karuwa ne sosai a cikin 2020 saboda an yi cinikin data har ta naira bilyan 332.416 a lokacin kullen korona da sauran watannin shekarar.
Shugaban Kamfanin MTN, Ferdi Moolman, ya ce cikin shekarar 2020 an samu gagarimin cinikin data, saboda kullen korona ya sa ma’aikata da dama su na yin akin su daga gida, ta hanyar amfani da data.