Gobara ta cinye Kasuwannin Katsina da Zamfara

0

Ibtila’in gobara ta afkawa manyan kasuwanne biyu a Jihohin Katsina da Zamfara a ranar Litinin da Lahadi.

Hukumomi a jihohin biyu sunce babu asarar rai da aka yi amma anyi asarar dukiyoyi na miliyoyin naira sakomakon wannan ibtila’in gobara.

A Jihar Katsina, anga yadda yan kasuwa suka kai dauki domin debe wasu daga cikin kayan shagon nasu a inda wutar bata kaiba.

Rahotanni sunce wasu sun suma sakamakon shakar hayaki a lokacin da suke yunkurin kawo dauki kayan nasu daga shago.

Shugaban Kasuwar ta Katsina Abbas Labaran, ya shaidawa manema labarai cewa har yanzu ba’a tabbatar da hakikanin abinda ya jawo gobarar ba. Yace wutar ta fara ci ne da safiyar litinin.

Jami’an yaki da gobara sun yi nasarar kashe wutar daga baya, amma tayi mummunar barna.

PREMIUM TIMES HAUSA ta ga yadda aka jibge jami’an tsaro bayan rahotannin wasu bata gari da ke balle shaguna suna sata bayan fakewa da cewa shagonsu ne.

Gwamna Aminu Masari, cikin gaugawa ya ziyarci kasuwar ya kuma Jajantawa shugabannin yan kasuwar da wadanda suka rasa dukiyoyin su.

Gwamna yace gobarar ita ce mafi mune a tarihin ibtila’in gobara a jihar ta Katsina. Yace hukumomi zasu fitar da bayanai kan irin asarar da akayi nan gaba kadan.

Ya kuma ce, gobarar zata bawa gwamnatin Jihar damar kara daura damara domin kiyayewa faruwar haka a gaba da kuma samar da abubuwan kare afkuwar gobarar a cikin kasuwar.

Gwamnati zata taimakawa wadanda sukayi asara, inji Masari.

Jihar Zamfara

A jihar Zamfara ma gobara ce ta lashe shaguna sama da 63 a babban kasuwa dake Tudun wada a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara a ranar Lahadi.

Gobarar ta auku ne sakamakon haduwar wayar wutar lantarki a wane shagon siyar da kayan sanyi.

Gwamnan Jihar, Bello Matawalle, ya jajantawa yan kasuwar. Yace kaddara ce daga Allah. Amma ya bada shawara ga yan kasuwa dasu rika kashe kayan lantarki bayan sun tashi daga kasuwa.

Matawalle ya kafa kwamiti su binciki irin asarar da akayi, yace gwamnati zata gina duk shagunan da gobarar ta lalata.

Share.

game da Author