GARGADIN BUHARI GA HAFSOSHIN TSARO: Ku murtsuke masu garkuwa da ’yan bindiga kowa ya huta

0

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa Manyan Hafsoshin Tsaro gargadi a ranar Talata cewa su gano shugabannin ’yan bindiga da masu garkuwa, kuma su murtsuke su baki daya a huta a kasar nan.

“Ku zabura haikan ku gani ’yan bindiga da masu garkuwa da masu kai masu rahoto, wadanda ke hada baki da su, domin ku murkushe su baki dayan su a kasar nan ta huta.”

Buhari ya bada wannan umarni yayin da ya ke shirin tashi daga Abuja zuwa London, inda ya yafi kai ziyara domin a duba lafyar sa.

Ya kira taron sjrri ne da manyan hafsoshin tsaro a Fadar Shugaban Kasa da ke Aso Rock Villa.

Mashawarcin Shugaban Kasa a Fannin Tsaro, Babagana Monguno, ya bayyana cewa Shugaban Kasa ya ba su wannan umarni actaron sirrin da ya kira manyan hafsoshin, kafin ya tashi zuwa London domin duba lafiyar sa.

Monguno ya shaida wa manema labarai a fadar Shugaban Kasa cewa, Buhari ya shaida wa manyan hafsoshin cewa ba zai lamunci a kullum sai dai a rika kai wa sojoji hari ba, sai bayan an kai masu hari su yi ta kokarin kare kai ko fatattakar masu garkuwa, ’yan Boko Haram ko ’yan bindiga ba.

“Batun garkuwa da mutane da hare-haren ’yan bindiga kuwa har yanzu ana ci gaba da fama da shi a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.

“Shugaban Kasa ya jaddda cewa lallai ya zama dole a kawo karshen wannan gagarimar matsala, ta hanyar amfani da hanyar da aka horas da sojoji sanin dabarun kawar da matsalar.

“Shugaban Kasa y ace aiki na farko da ya fara wajaba kan sojojin shi ne su gano manyan shugabannin masu garkuwa, su murtsike su domin jama’ar yankunan su sake gamsuwa da hakkin tsaron su da kula da rayuwar su da gwamnati yi.

PREMIUM TIMES HAUSA ta buga labarin alwashin da Babban Hafsan Askarawan Najeriya, ya jaddada cewa sojojin Najeriya za su kwankwatse duk wata barazanar da matsalar tsaro ke wa kasar nan.

Cikin labarin, Babban Hafsan Askarawan Najeriya, Janar Ibrahim Attahiru, ya bayyana cewa sojojin Najeriya za su ci gaba da kasancewa gudumar kwankwatsar duk wata barazana da matsalar tsaro ke wa kasar nan.

Ya ce za su ci gaba da jajircewa wajen aikin dakile duk wata barazanar tsaro, kamar yadda Shugaba Muhammadu Buhari ya ba su umarnin ci gaba da yi.

Attahiru ya yi wannan jawabin kara karfin guiwa a lokacin da ya ke bayani wajen bude taron sanin-makamar-aiki na watanni ukun farkon shekarar 2021, wanda ofishin sa ya shirya wa jami’an sojoji, ranar Litinin a Abuja.

Ya ce Sojojin Najeriya su na da himma da jajircewa wajen ganin sun bi dukkan umarnin da Buhari ya ba su domin yi wa dukkan wata barazanar tsaro dukan-kabarin-kishiyar da za a magance matsalar baki daya.

Attahiru ya kara da cewa wannan taron sanin-makamar-aiki na watanni ukun farkon shekarar 2021, zai bayar da wata kafa da damar sake nazarin irin barazanar da yanayin wurare ke haifarwa wajen gudanar da ayyukan sojoji a sassa daban-daban.

Ya ce idan aka yi wannan nazari, za a kara gano wasu nakasu ko gibin da su ka kamata a gaggauta cikewa tare da shawo kan su ta hanyar tsare-tsaren da ake kan shirin yi a fafatawar da za a ci gaba nan gaba.

“Ina kara jaddada cewa Sojojin Najeriya a karkashin kulawa ta za su ci gaba da kasancewa masu kwankwatsar duk wata barazanar matsalar tsaro a kasar nan.

“A kan haka ina umartar dukkan cewa a rika maida hankali sosai wajen ganin ana ci gaba da samun irin gagarimar nasarar da mu ke kan samu a yanzu, har ma mu kara kaimin ganin samun fiye da wadda mu ke samu din a yanzu.

“Dukkan kwamandojin da ke bakin daga tilas su rika tilawar umarnin da na bayar wajen tabbatar da tilawar a aikace domin kara samun nasara tare himmar gaggauta kawar da duk wata barazana.”

Share.

game da Author