Majalisar Tarayya ta bayyana cewa fatara da matsanancin karancin kudade sun addabe su da majalisar baki daya, har ta kai ba su iya gudnarwa da aiwatar da wasu ayyukan da tsarin mulkin Najeriya ya wajabta masu yi a kasar nan.
Kakakin Yada Labarai na Majalisar Tarayya, Benjamin Kalu, dan APC daga Jihar Abia ne ya bayyana haka a ranar Alhamis, yayin taro da manema labarai.
Daga nan said an majalisar ya bayyana cewa ya kamata a sake duba kasafin kudi na 2021, ta yadda za a kara masu wadatattun kudaden da za su ishe su gudanar da ayyukan da su ka rataya a kan su.
An dai ware wa Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya naira bilyan 128 a Kasafin Kudin 2021. Sannan kuma naira 125 aka ware masu a Kasafin 2020.
“Tabbas Majalisa ta shiga cikin mawuyacin halin fatara. Na taba bayyana haka a baya, kuma yanzu ma ina kara bayyana maku hakan. Saboda ni dai ba tsoron bayyana haka na ke yi ba.
“Wannan batu nawa gaskiya ne. Ya kamata ’yan Najeriya su sani cewa fa shi wannan kasafi an tsara mana shi tun ana canja dala daya kan naira 180.
“Amma a yau ana canja dala daya naira 400, kun ga kenan karfin kasafin kudin ya susutar da karfin naira, ba kamar shekaru 10 baya ba.” Inji Honorabul Kalu.
“Me ya sa ba za ku iya fitowa ku kwatar mana ’yanci ku kara yawan kasafin kudin majalisa domin mu rika gudanar da ayyukan mu kamar yadda doka ta ba mu izni da karfin iko ba?”
Kalu ya ce sai da ya kai ruwa rana da shugabannin majalisa, ya ce tsoron me su ke ji da ba za su iya fitowa su yi magana ba?
“Mu ne fa ke amincewa da kasafin kudin hukumomi yadda zai wadace su gudanar da ayyukan su. To don me za mu yi wa kan mu kwange?”
Discussion about this post