A daidai lokacin da Najeriya za ta fara gwanjon wasu kadarorin Gwamnatin Tarayya domin samun kudin shiga, kuma a daidai lokacin da kasar nan ke ci gaba da ciwo bashi malala-gashin-tunkiya, a lokacin ne kuma wannan gwamnatin za ta fara aikin yi wa Majalisar Kasa kwaskwarimada naira biliyan 42.
Tun farko dai mafi yawan ’yan Najeriya sun nuna kin amincewar su da kudaden da aka ware a cikin kasafin kudi domin a yi wa majalisar kwaskwarima.
Sai dai kuma wannan kuka da korafi na mutane bai shiga kunnuwan gwamnatin Buhari ba, domin aikin kwangilar kwaskwarimar na nan daram za a fara.
Naira biliyan 42 da gwamnati za ta yi wa ginin majalisa kwaskwarima da su dai sun zarce kasafin kudin da gwamnatin tarayya ta ware wa Babban Asibitin Koyarwa na Jam’iar Legas, kuma ya zarce kasafin da aka ware wa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos ko na Jami’ar Ibadan ko wasu kananan asibitocin da ke aikin ceto rayukan ’yan Najeriya dare da rana.
An bai wa kamfanin ‘Visible Consturucton Limited’ kwangilar yi wa majalisar kwaskwarima, wanda hukumar tantance farashin kwagiloli (BPP) ta amince da kudaden ta tare da bayar da takardar shaidar amincewa.
Idan ba a manta ba, Gwamnatin Buhari za ta ciwo bashin naira tiriliyan 5.6 doin aiwatar da ayyukan kasafin kudi na naira tiriliyan 13.6 a 2021.
Sannan ba a dade da fita daga kangin matsin tattalin arziki ba, ga matsalar hauhawar farashi da kuma matsalar asarar da ake tafkawa wajen shigo da tattaccen man fetur daga kasashen waje.
Ko cikin makon jya dai gwamnatin Buhari ta bayyana cewa za ta kashe naira bilyan 600, domin gyaran matatar danyen an fetur ta fatakwal, kalamin da ’yan Najeriya da dama su ka yi tir da shi.
Sannan kuma kwanan baya Najeriya ta bayyana cewa matsalar rashin kudi za ta sa gwanatin Buhari cin bashi kudaden da masu ajiya su ka ajiye a bankuna tsawon lokaci ba su taba ko su ka juya su, ko su ka karba ba.
Ko kwanan nan gwamnati ta nanata wannan kokarin fara karbar kudaden a matsayin ramce domin a samu kudaden da za a aiwatar da ayyukan raya kasa da aka yi alkwari a cikin kasafin 2021.
Wannan shiri ma dai jama’a ba su amince da shi ba.
Discussion about this post