Kamfanin Dangote Sugar Refinery, ya bayyana cewa cinikin da ya samu na sukari a shekarar 2020, ya karu da naira bilyan 53, idan aka kwatanta da cinikin shekarar 2019.
Wannan gagarimin ciniki kamar yadda kamanin ya nuna, ya karu ne sakamakon fito da babban buhun sukari mai nauyin 50kg da aka yi.
Arankatakaf dai Dangote Sugar ya yi cinikin naira bilyan 214.998 a cikin shekarar 2020, kuma kashi 49 bisa 100 na wannan cinikin, duk a Lagos aka yi shi.
“Wannan kudin shiga sun karu ne saboda fito da babban buhu mai nauyin kilo 50kg, wanda a shi kadai aka yi cinkin naira bilyan 206.444, ko kuma a ce kashi 96 na cinikin sukarin Dangote na 2020, duk daga cinikin babban buhun sukari aka same su.
PREMIUM TIMES ta yi tozali da jadawalin ciniki da kasuwancin masana’antar sukari ta Dangote, na shekarar 20202 a ranar Talata.
Cikin shekarar 2020, Dangote Sugar wanda shi ne babbar masana’antar yin sukari a Afrika, ya kara bunkasa ta hanyar hadiye kamfanin sukari na Savannah Sugar da ya yi, wanda ke Adamawa.
Hakan ne ya sa a shekara ha rake iya samar da karin sukari na tan 50,000 kowace shekara.
A bangaren sukari, Dangote ya samu ribar naira bilyan 29.775. Kenan ribar 2020 ta haura ta shekarar 20219 da aka samu naira bilyan 22.361.
Discussion about this post