Fitaccen jarumin finafinan Najeriya Pete Edochie ya bayyana wasu dalilai da ya sa mata ke yi wa mazajen su rashin kunya da tsagalgalewa ba tare da yun ta’akari cewa suna karkashin su bane.
Edochie ya ce idan bera da sata, daddawa ma da wari, yana mai cewa mazan yanzu malalata ne ba kamar mazan da ba da ke da kwazo matuka.
Ya ce idan har mace za ta iya canja sunan mahaifinta ta musanya da na mijinta saboda aure hakan ma ai biyayya ne.
Edochie ya ce lokacin da ya yi aure mata na da ladabi da biyayya sannan ba za su taba yi wa mazajen su rashin kunyi ba kamar yadda matan wannan zamani ke yi a fili ba.
“A zamanin mu mata na zama abin sha’awa saboda ladabi da biyayyar da suke yi wa mazanjen su ba kamar yanzu ba da mata sun zama masu jiran ko ta kwana.
Da ma kuma Edochie ya taba yin kira da gargadi ga maza su daina biye wa matan su suna binsu kamar sune masu gida maimakon uwargida.
Ya hori mutane su guje wa yin biyayya ga al’adun da ba na su ba.
Discussion about this post