Dalilin da ya sa Kotu ta dakatar da yin muƙabala bayan Abduljabbar ya kammala shirin karawa da malaman Kano

0

A yanzu dai wata kotu a Kano a ranar Juma’a ta dakatar da yin mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Kabara da wasu gungun malaman Kano.

Dama kuma kafin kotun ta dakatar da mukabalar, har zuwa ranar Juma’a ba a ji sunayen zaratan malaman da su ka yi balantiyar fitowa gwabza karo da malamin wanda ke kalubalantar wasu maganganun da aka jingina ga Annabi (SAW) wasu littatafan magabata.

PREMIUM TIMES Hausa ta ga bidiyon yadda hadiman Abduljabbar ke ta kai da kawon tattara littattafan da ya yi niyyar zuwa da su wurin mukabalar, wadda aka shirya gwabzawa a Fadar Sarkin Kano Aminu Bayero, a ranar Lahadi mai zuwa.

Haka nan kuma ta samu hotunan tulin damman littattafan, bayan an tattara su an daure su kashi-kashi.

Gidan Radiyon BBC ya ruwaito cewa, “ranar Juma’a ne Mai Shari’a Muhammad Jibrin na Kotun Majistire da ke Gidan Murtala, ya yanke hukuncin sakamakon bukatar da wani lauya mai zaman kansa Barista Ma’aruf Yakasai ya shigar gabanta.

“Barista Yakasai dai ya buaci a dakatar da gwamnati daga yin mukabalar ne, saboda hakan ya ci karo da umarnin da kotun ta bayar tun da fari na hana Sheikh Abduljabbar karatu da kuma saka karatukan sa a daukacin kafofin yada labaran jihar.

Haka nan kuma kafar yada labaran ta ruwaito cewa, “Gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta bi wannan umarni na kotu, inda Kwamishinan Shari’a Barista Musa Lawan ya yabbatar da cewa babu mukabala a ranar Lahadi mai zuwa.”

Lauyan Barista Ma’aruf wato Barista Lukman Auwalu Abdullah ya ce sun ji dadin umarnin kotun.

“Ya kara da cewa abin da ya sa Barista Ma’aruf ya shiga cikin lamarin shi ne saboda ya tunatar da dukkan bangarorin cewa bai kamata a yi mukabala ba, duba da umarnin kotun na farko na haramta wa Abduljabbar karatu.

“A ganin sa yin mukabalar tamkar an bar shi ya yi karatun ne wanda hakan soke umarnin kotun ne da yi mata rashin biyayya.”

An tsaida ranar 22 ga Maris don sauraren rokon Barista Ma’aruf Yakasai kan dukkan bukatun.

Kafin kotu ta dakatar da mukabalar, PREMIUM TIMES ta buga labarin yadda Sarkin Musulmi Saad Abubakar III ya bayyana cewa ba zai halarci mukabalar ba, kuma bai goyi bayan a yi ba, saboda hakan zai kara wa Abduljabbar suna.

A ranar Alhamis ce dai Jama’atu Nasril Islam a madadin Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, ta bayyana janyewar ta daga halartar makabala da Sheikh Abduljabbar Kabara a Kano.

JNI ta bayyana wannan matsayi na ta a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Kungiyar, Khalid Aliyu ya fitar, wadda ya aika wa PREMIUM TIMES ta hanyar sakon e-mel a ranar Alhamis.

Gwamnatin Jihar Kano dai ce ta shirya yin makabalar bayan da gamayyar malaman Izala, Salfiyyah, Tijjaniya da Qadiriyya su ka kai karar Abduljabbar ga Gwamna Abdullahi Ganduje.

Sun kai karar sa bisa zargin ya na tozarta wasu sahabbai da kuma yi wa wasu hadisan Annabi (SAW) baudaddiyar fahimta.

Dama malamin ya sha neman su zauna a yi makabala da malaman na Kano.

Bayan da Gwamna Ganduje ya hana shi karatu, tare da rufe masallacin sa da rushe makarantar sa, ya nemi a hada shi makabala da malaman, domin a ga wanda ke kan daidai da wanda ke kan kuskure a tsakanin su.

Sai dai kuma bayan Ganduje ya yi sanarwar amincewa a yi mawabala, sai wasu malaman Izala su ka rika cewa babu amfanin a yi zaman makabala da malamin, wanda ke kiran bangaren sa ‘Ashabil Kahfi War Raqeem’.

Share.

game da Author