Dalilan mu na neman a dage wa Sheikh Abduljabbar dokar hana shi wa’azi –Majalisar Malaman Musulunci

0

Majalisar Malaman Musulunci ta Najeriya, wadda aka fi sani da suna Nigeria Council of Ulama, ta bayyana dalilan da ya sa ta nemi Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya yi adalci ya kyale Sheikh Abduljabbar ya ci gaba da wa’azi, tare da bude masa masallacin sa.

Cikin wani taron maneman labarai da ya shirya A Bauchi Sheikh Dan’azumi Tafawa Balewa ya bayyana cewa a ka’idar shari’a ko ta dimokradiyya ko ta musulunci, ba a karbar shaidar abokin gaba ko abokin abokin adawa, har sai an ji ta bakin wanda ake kara, sannan ake yi adalci wajen yanke hukunci.

Dan’azumi wanda ya bayyana cewa shi ne mataimakin Shugaban Majalisar Malaman, amma yanzu ya na zaman shugaba ne, domin shugaban ta Abubakar Tureta ya rasu.

Ya nuna rashin jin yadin yadda wasu gungun malamai su ka matsa wa Gwamna Ganduje lamba, har ya rufe masallaci tare da hana Abduljabbar wa’azi.

Ya ce ba wani abu ba ne sai nuna hassada kawai, saboda ya tsare masu gaba, kuma ya na ƙara haska wa jama’a hanyar da jama’a ke kara karbuwa a hannun sa, su na barin wadancan malaman.

Dan’azumi ya ce dokar Najeriya ta bai wa Sheikh Abduljabbar ‘yancin yin wa’azin sa, kamar yadda ta bai wa sauran malaman. Abin da kawai ya rage wa sauran musulmai shi ne kowa ya bi wanda ya ke so.

“Shi ma addinin musulunci ya ce babu tilas wajen tirsasa wani ya bi wani addini. Don me wadannan gungun malaman za su ce sai koyarwar su kadai za a bi? Inji shi.

Shehin malamin wanda ya ce shi dan darikar Tijjaniyya ne, ya yi karin hasken cewa an kafa Kungiyar Malajisar Malaman Musulunci cikin 1980, a karkashin mabambantan aƙidu bisa jagorancin marigayi Hassan Gwarzo, domin fahimtar juna.

Sannan kuma ya kara da cewa bai ji dadin da aka hana yin maqabala ba, domin babu aibi wajen yin maqabala, tunda sahabbai ma sun yi maƙabala kuma sun fahimci juna daga baya. Inji Dan’azumi.

Cikin bidiyon minti 40 da aka nuno shi ya na jawabi, malamin ya rika buga misalai da ayoyin Alkur’ani, wadanda ya rika jawo wa Ganduje cewa ya yi adalci.

Sannan kuma ya riƙa kawo hadisai da su ka nuna an yi tankiya tsakanin sahabbai, kuma an maƙabala, daga baya an fahimci juna, har a tsakanin manyan sahabban Annabi sallallahu alaihi wasallam su hudu.

Ya ce muddin za a ce da wasu gungun malamai sun hadu sun kai kuka wurin gwamna, shi kuma ya biye masu ya hana wani malami wa’azin sa, to wannan an dora al’umma kan makauniyar turbar da nan gaba duk rashin gaskiyar wasu malamai za su iya hada kai su tunkari gwamna ya biya masu bukatun su.

Jama’a da dama dai sun nuna rashin jin dadin dakatar da maƙabala, inda wasu ke ganin cewa da malaman da su ka kai karar Abduljabbar wurin gwamna su na yakinin yin galaba a kan sa, to da sun shiga sun fita sun tabbatar da cewa an yi maqabalar, ko don su kashe bakin tsanya.

Share.

game da Author