Dalibai 279 ne aka sace kuma duk an dawo da su, ko sisi ba mu biya ba – In ji Matawalle

0

Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya tabbatar da dawo da daliban makarantar Jangebe da ‘yan bindiga suka sace a makon jiya.

A hira da gwamna matawalle yayi da Radiyon Tarayya kai tsaye a safiyar Talata, ya ce dalibai 279 ne aka sace ba 317 da ake ta ruwaito wa ba.

” Ba mu biya ko sisi ba wajen karbo daliban makarantar Jangebe ba saboda haka idan ma wasu na ganin wai sai da muka biya wani abu, can ta matse musu. Mu dai ba mu biya ko sisi ba.

” Daliban da aka sace duk mun dawo da su. Wa su daga cikin su na can likitoci na duba su, Ana kuma basu abinci. Za a kai su su huta su yi barci tukunna kafin a mika su ga iyayen su.

Share.

game da Author