Akwai wani kakkausan kalami da dattijo Buba Galadima ya yi a farkon shekarar 2021, inda ya rantse da Allah ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari ba zai bai wa Jigon Jam’iyyar APC, Bola Tinubu tutar takarar shugaban kasa a zaben 2021 ba.
Kafin wannan kalami na Galadima, da dadewa kowa ya san yadda Tinubu ya zama dodon kodi bayan nasarar da APC ta samu a zango na biyu.
Ya zama dodon kodi, ta yadda ya noke ya koma cikin gida, ya koma gefe, na a jin sa ko ganin sa a batutuwa na siyasar kasar nan, sha’anonin da su ka jibinci masu mulki da kuma dangane da irin matsanancin halin da ake ciki a kasar nan.
Yayin da tuni wasu yaran siyasar sa da makusanta da kafafen yada labarai ke ci gaba da nuna bukatar Tinubu na tsayawa takarar shugaban kasa zaben 2023, an wayi gari ya rufe bakin sa na ya cewa komai a kan abubuwan da ke faruwa a kasar nan.
Ko a yayin tarzomar #EndSARS, Tinubu bai yi magana sosai ba. Haka nan a rikicin Hausawa da Yarabawa a Kasuwar Shasha da ke Ibadan, nan ma Tinubu bai fito ya tsawatar, a matsayin sa na dattijon Yankin Yarabawa ko jigon APC mai mulki ba.
Yayin da rikicin korar Fulani makiyaya daga jihohin Yarbawa ya tirnike, ba a ji wasu zafafan kalaman yin tir daga bakin Tinubu ba.
Jagaban wanda ya yi namijin kokarin ganin Buhari ya lashe zabe a 2015 da 2019, a yanzu sai a dade ba a ji duriyar sa a Fadar Shugaban Kasa ba. A baya da wuya Buhari ya je taron da ya shafi APC ba tare da ya ambaci sunan Tinubu ya na jinjina masa ba.
Amma a yanzu kuwa har mantawa ake yi a ji Buhari ya ambaci sunan Tinubu. Shi kan sa Tinubu din ba ya cewa komai, kowa ya daina jin duriyar sa.
Sai dai kuma daidaikun jama’a na nan na ci gaba da yi wa Tinubu sharar-hanyar tsayawa takarar shugabancin kasar nan a zaben 2023.
Za a iya cewa sa-in-sar da ake yi yanzu tsakanin ‘yan Arewa da Kudu, bayan rikicin Kasuwar Shasha da korar Fulani za su iya kawo wa Tinubu tawaya ga kokarin sa na tsayawa takara. Da yawa daga Arewa sun fara jefa wa duk wani dan takarar shugabancin kasa daga kudu alamar tambaya a kan su.
Ya ci a ce Tinubu ya fito ya yi kiran sasantawa da manyan masu safarar kayan abinci yan Arewa, wadanda su ka hana kai kayan abinci kudancin kasar nan. Amma Tinubu bai ce komai ba.
Haka batun yawan save mutane ana garkuwa da su, nan ma ba a ji kakkausar murya daba bangaren Tinubu ba.
Yayin da had yanzu ba a kai wurin tsayar da dan takara ba tukunna a kowace jam’iyya, abubuwa da dama su na ta faruwa a kasar nan kamar Tinubu bai san su na faruwa ba kwata-kwata. Wannan kuwa ba hanya ce mai bullewa ga dan siyasa, ko da kuwa dan jagaliyar siyasa ne. Ballantana kuma kasaitaccen jigon APC irin Tinubu.