Dubban magoya bayan tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu ne suka yi dafifi a filin jirgin saman Kano domin yi wa jagoran APC din lale maraba da zuwa wani taro da za a yi domin bikin zagayowar ranar haihuwar sa.
Tinubu ya cika shekaru 69 a duniya kuma shine akan gaba wajen musanya Buhari a 2023.
Dubban Jama’a sun yi dafifi a Kano wasun su bisa babura suna cewa ” Daga Buhari Sai Tinubu”.
Wani dan gani kashenin Tinubu a Kano, Haruna ya ce mara wa Tinubu baya a Kano ya zama tilas saboda tsayawa kem da yayi tare da shugaba Buhari ba dare ba rana. Duk da mun san ba ya taho Kano domin yin Kamfen bane, mun fito ne domin mu nuna masa cewa a Kano fa Tinubu kawai ake yi.
Shi ko Ibrahim Dahiru cewa yayi ” A siyasance Tinubu dan Arewa ne domin a kullum yana tare da Arewa kuma ya yi wa Arewa halasci musamman wajen tsayawa tsayin daka ya tabbata Buhari ya samu karbuwa a yankin Kudu Maso Yamma da irin kauna da ya nuna wa Buhari a tsawon shekarun da suka yi suna mulki.
Za a yi taron jawabai na Tinubu Colloquium a garin Kano sannan zai samu halarcin shugabannin kasashen Afrika da dama da gaggan yan kasuwa da yan boko na ciki da wajen nahiyar Afirka. Shima shugaba Muhammadu Buhari zai halarci taron a ta yanar gizo.