Da in karya dokar kasa, ko a tilasta ni in yi abinda ba haka ba, gara in ajiye aikin – Bawa

0

Shugaban Hukumar EFCC Abdulrasheed Bawa, ya bayyana cewa zai yi aiki cikin gaskiya da kiyaye dokar Kasa.

Ya ce da ya karya doka ko ya bi son rai gara ya ajiye aikin sa kawai ya hakura.

Bawa ya yi karin haske game da umarnin da hukumar ta bayar kan kowani ma’aikacin banki ya bayyana kadarorin sa da duk abinda ya mallaka ga hukumomi domin asan me kowani ma’akaci ya mallaka.

” A nan ba wai muna cewa sai sun bayyana kadarorin su ga hukumar bane, a’a za su bayyana ne ga wata hukuma, wanda ga wannan hukuma ce za mu binciki abin da kowani ma’aikaci ya mallaka.

Ya ce doka ta ba da damar haka.

” Sannan kuma muna yin kira ga yan Najeriya su daina karrama yan Najeriyan da suka tara kudin haram. Ya ce ba kowane mai arziki bane ya same su ta hanyar kwarai.

Bawa ya ce hukumar zata cigaba da wayar wa mutane kai kan yadda za su rika kiyaye wa daga tsumbula hannayen su cikin dukiyar da ba na su ta hanyar zamba, sata ko damfara.

A karshe Bawa ya ce hukumar za ta cigaba da aiki da kafofin yada labarai domin ba yan Najeriya daman sanin abinda ya kamata su sani game da hukumar da kuma ayyukanta. Sannan kuma da ba kowa damar bincikar kararrakin dake kotunan kasar nan musamman yan jarida.

Share.

game da Author