CIN HAKKIN MARAYU DA NAKASASSU: Naira milyan 148 sun ja wa tsohon minista zama kwanaki 25 a hannun EFCC

0

Hukumar EFCC ta gurfanar da tsohon Ministan Makamashi, Muhammad Wakili, wanda ta ke zarge da laifuka biyu da su ka jibinci rashawa da cin hanci.

An gurfanar da Wakili a Babbar Kotun Tarayya da ke Apo, Babban Birnin Tarayya, Abuja, ranar 8 Ga Maris, 2021, bisa zargin sa da karbar naira milyan 148 daga wasu kudaden inshorar wasu ma’aikatan Hukumar Bada Wutar Lantarki ta Kasa (PHCN).

Kudaden dai na ma’aikatan da su ka mutu ne da kuma hakkin wadansu da su ka ji rauni ko ba su iya amfani da karfin su domin amfana wa kan su wani abu.

Mai gabatar da kara ya shaida wa kotu cewa cikin 2014, tsohon minista Wakili ya kamfaci naira milyan 148 wadanda hakki ne na wasu tsoffin ma’aikatan da su ka mutu da kuma na wasu nakasassun tsoffin ma’aikatan Hukumar PHCN, wato tsohuwar hukumar bada wutar lantarki ta kasa.

An yi zargin ya karbi kudaden ta hannun kamfanin Inshora na Bestworth Insurance Brokers Nigeria Ltd.

An ba shi kudaden ta hannun asusun ajiyar kamfanin sa, wato Corozzeria Nigeria Ltd.

Sai dai kuma yayin da aka karanto masa laifukan da ake zargin ya aikata, ya musanta, tare da cewa bai ci ko sisi ba.

Sai dai kuma Mai Shari’a S.B Belgore ya umarci EFCC su ci gaba da rike shi a hannun su, har sai ranar 31 domin a fara maganar bada beli tukunna.

“Kai Wakili ana zargin ka karbi rashawar naira milyan N148,000,000.00 daga Bestworth Insurance Brokers Limited daga cikin naira bilyan N27,188,232,208.00, wadanda kudaden inshora ne hakkin iyalan ma’aikatan Hukumar PHCN da su ka mutu da kuma wadanda su ka samu nakasa a jikin su.”

Lauya mai gabatar da kara Benjamin Manji ya roki kotu ta sa ranar fasa shari’a, kuma ta ajiye tsohon ministan kurkuku kafin ranar.

Sai dai kuma lauyan Tsohon Minista Wakili, mai suna B.C Igwilo, ya nemi a saka batun Wakili cikin hurumin bayar da beli.

Amma dai shi kuma Mai Shari’a Belgore ya ce EFCC ta ci gaba da tsare shi, sannan a koma kotu ranar 31 Ga Maris, domin duba batun beli, kafin daga nan kuma a fara shari’a.

Share.

game da Author