CETO DALIBAN KADUNA: Buhari ya jinjina wa gwamnatin Kaduna da Sojoji

0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yaba wa Gwamnatin Kaduna da sojojin Najeriya kan ceto mutane 180 da masu garkuwa da mutane su kayi.

Idan ba a manta ba ‘Yan bindiga sun sace dalibai da wasu daga cikin malaman makaranta fasahar raya gandun daji da ke Kadunaranar Juma’a.

Sai dai tun kafin maharan su yi nisa da daliban cikin kungurmin daji jami’an tsaro su ka sawun su suka ceto dalibai da wasu har 180.

Shugaba Buhari ya umarci jami’an tsaro su tabbata sun ceto sauran daliban.

A karshe shugaba Buhari yabawa ‘yan banga da suka taimaka da bayanan sirri wajen ceto daliban.

Har yanzu dai akwai mutum 39 da ke tsare haryanzu a hannun’ yan bindiga.

Share.

game da Author