Buhari zai tafi ganin likita Landan – Fadar Shugaban Kasa

0

Kakakin fadar Shugaban Kasa Femi Adesina, ya bayyana cewa shugaban Kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Birtaniya domin duba lafiyar sa.

Wannan sanarwa ta fito daga fadar gwamnati ranar Litinin.

Ana sa ran shugaba Buhari zai shafe makonni biyu a Landan wajen ganin likita kafin ya dawo Najeriya.

Shgaban Kasa Muhammadu Buhari ya kwana biyu bai fice daga Najeriya ba tun barkewar annobar Korona a 2020.

Share.

game da Author