BIN-DIDDIGI: Kashi 1 bisa 3 na Ministocin Buhari duk daga jami’a daya su ka fito

0

Wani bin-diddigi, wai kuturta bin dan kishiya, ya tabbatar da cewa Ministocin Shugaba Muhammadu Buhari 13 daga cikin su 44, duk tsoffin daliban Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ne (A.B.U).

Yayin da takwas daga cikin sauran kuma duk sun fito ne daga Jami’ar Lagos.

Sannan kuma 18 daga cikin su 44 din duk a manyan makarantun kasashen waje su ka yi digirin su daban-daban.

Jami’ar Ahmadu Bello dai bana shekarar ta 58 da kafawa, inda a farkon kafuwar ta, aka rada mata suna University of Northern Nigeria, wato Jami’ar Arewacin Najeriya.

Ministan Babban Birnin Tarayya Abuja, Muhammad Bello, shi a kasar Sudan ya yi digirin farko da na biyu a jami’ar a fannin tsarin kasuwanci, a 1980 da kuma 1987, ya je Jami’ar International University of Africa da ke Sudan ya yi digiri cikin 1994.

Ita kuwa Karamar Ministar Muhalli, Sharon Ikpeazu, ta halarci ABU cikin 1981, inda ta yi jarabawar shiga Jami’a, wato IJMB.

Ministocin Buhari da su ka halarci ABU sun hada da Minstan Harkokin Ilmi, Adamu Adamu, Karamar Minsitan Masana’antu, Maryam Katagum, Karamin Ministan Makamashi, Goddy Jedy Agba, Ministan Harkokin Ruwa, Suleiman Adamu, Ministar Harkokin Kudade, Zainab Ahmed da kuma Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono.

Sauran sun hada da Ministan Tsaro, Bashir Magashi, Karamar Ministar Babban Birnin Tarayya Abuja, Ramatu Tijjani, Karamin Ministan Harkokin Kasashen Waje, Zubair Dada, Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Maigari Dingyadi da kuma Ministar Agaji, Jinkai da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, Sadiya Faruk.

Wani dalibin ABU da ya kammala digirin farko cikin shekarar 2018, kuma ya samu makin da mai digiri na farko dai taba samu ba tun farkon kafa jami’ar shekaru 58 da suka gabata (maki 4.94), ya bayyana wa PREMIUM TIMES cewa watakila hakan ta kasance ne saboda dadewar da ABU ta yi wajen kwarjini da kuma zalaka, shi ya sa har ta samar da ministoci 18 a cikin ministoci 44 na Buhari.

A yanzu Nura ya na Jami’ar Manchester a Ingila, ya na karantar digirin sa na biyu.

Tsoffin daliban Jami’ar Lagos ne na biyu wajen yawa, har su 8 a cikin ministicin Shugaba Buhairi.

Wannan ya nuna kenan Ministoci 26 daga cikin 44 na Buhari, sun fito ne daga jami’o’i biyu, wato Jami’ar Ahmadu Bello da Jami’ar Lagos.

Share.

game da Author