Gwamnatin jihar Zamfara ta saka dokar hana walwala tun daga karfe 6 zuwa dare a garin Jangebe.
Gwamnati ta yi haka ne a dalilin barkewar rikici da wasu masu zanga-zanga suka fara a garin.
Kwamishinan yada labarai na jihar Sulaiman Anka ya sanar da haka ranar Alhamis.
Ya ce matasa masu zanga-zanga sun tada rikicin ranar Laraba bayan gwamnati ta maido daliban makarantar sakandaren Jangebe da aka yi garkuwar da su a makon jiya.
” Matasa masu zanga-zanga sun tarwatsa wani taro da gwamnati ke yi da iyayen dalibai a makarantar ranar Laraba a Jangebe.
“Matasan sun yi wa wasu jami’an gwamnati ruwan duwatsu harda kakakin majalisar dokokin jihar Nasiru Magarya.
A makon da ya gabata PREMIUMTIMES HAUSA ta buga labarin yadda matasan garin Jangebe suka rika yi wa motocin gwamnati ruwan duwatsu da Kai wa ‘yan jarida hari domin nuna gazawar gwamnati na samar musu da tsaro a yankin.
Matasan sun gudanar da zanga-zanga bayan sace daruruwan dalibai mata ‘yan makaranta da aka yi a Jangebe, karamar hukumar Talatan Mafara.
Matasan sun tattare mashigar garin Jangebe don hana duk wani jami’in gwamnati shiga gari,
Duk wanda ya tunkaro sai ya ji ruwan duwatsu ta ko-ina. A haka dai har wasu sun samu rauni, wasu motoci kuma sun fada tarkon matasan.
Bayan an ceto yan makarantar, Buhari da ya gargadi yan bindiga da suka maida sace daliban makaranta sana’ a da masu basu goyon baya su shiga taitayin su, cewa gwamnati ba zata lamunta wa duk wanda aka samu da hannu a aikata wannan mummunar abu ba.
Discussion about this post