Gwamnan Jihr Rivers ya yi korafin cewa Babban Bankin Najeriya, CBN ya hana jihar sa lamunin bunkasa harkokin noma da bankin ke raba wa a wasu sassan kasar nan kamar tuwon-gayya.
Wike ya ce abin mamaki kuma abin takaici a kasar da ke amfani da tsarin federaliyya, amma a rika kwasar kudin kasa ana fifita wani bangare da su, da sunan ba su lamunin bunkasa noma, amma kuma saboda bambancin siyasa a hana wata jihar wannan damar.
Gwamna Wike ya yi wannan korafin a lokacin da Karamin Ministan Gona, Mustapha Shehuri ya kai masa ziyara a ofishin sa a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas.
Wike ya ce siyasa ta yi katutu a CBN wajen rabon kudin tallafi ko lamunin bunkasa harkokin noma da bankin ke bayarwa.
“Jihar Ribas na daya daga cikin jihohin da CBN ya hana lamunin bunkasa harkokin noma. Wannan kuwa kwata-kwata rashin adalci ne, bai kamata a rika sa siyasa a harkar lamuni ga jama’ar karkara na kasar nan.”
Ya kara da cewa kamata ya yi a ce CBN ta hada kai da gwamnatocin jihohi wajen bayar da wannan lamuni ga manoman kowace jiha, maimakon ta ware wasu jihohi ta na ba su lamunin, wasu jihohin kuwa saboda bambancin siyasa, kiri-kiri ana hana su.
“Wannan lamunin bunkasa harkokin noma fa shiri ne da zai bunkasa abinci, ya samar da aikin ga dimbin matasa kuma ya inganta rayuwar su.
“Idan har gaskiya ake son aikata, bai kamata a tsarma siyasa a wannan harka ba. Ya kamata a ce mu na aiki kafada-da-kafada domin mutanen mu su ma su amfana da wannan lamuni.” Inji Wike.
Tun da farko Minista Shenuri ya ce ya je jihar Ribas ne domin ganin yadda wani aikin bunkasa harkokin noma ke gudana.
“A shirye mu ke su tallafa wa manoman jihar Ribas da sabbin kayan aikin noma na zamani, kuma a inganta duk wasu hanyoyi da aka tabbatar idan aka bi, za a samu bunkasar noma sosai a jihar Ribas.” Inji Shehuri.