BADAKALA: Ana binciken yadda aka yi wa gangar danyen mai milyan 5.2 shan ‘pure water’ cikin 2018

0

Yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ne Ministan Man Fetur na Najeriya, abin mamaki ya faru, inda Majalisar Tarayya ta bankado yadda aka karkatar da danyen man fetur ga wasu matattun matatun mai har ganga milyan 5.2 a cikin shekarar 2018.

A ranar Laraba din nan ce Majalisar Tarayya ta umarci Kwamitin Lura da Harkokin Mai ya binciko yadda aka yi wannan harkalla a cikin 2018, inda aka sayar wa matatun man, wadanda aka tabbatar da cewa a mace su ke murus danyen man fetur mai tarin yawa.

An yi wannan kasuwanci ne bisa tsarin sayawa kai tsaye, saye kai tsaye, wanda aka shigo da shi cikin 2016.

A karkashin tsarin, ana sayar da danyen man ga masana’antun tace mai, su kuma su rika bai wa Hukumar NNPC wasu nau’o’in albarkatun mai da ake tacewa daga danyen man fetur din.

A karkashin wannan tsari dai NNPC ce kadai ke da ikon shigo da tataccen man fetur cikin kasar nan.

Dan Majalisar Tarayya, Makki ne ya tayar da maganar a matsayin wani kudiri da ya gabatar a Majalisa a ranar Laraba.

Ya nemi Majalisa ta binciki yadda cikn 2018 aka bayar da danyen man fetur din har ganga milyan 5.2 ga wasu tsoffin matatun mai na cikin gida, wadanda shekaru aru-aru da yin jana’izar su.

Wannan lamari dai ya faru a lokacin da Shugaba Muhammadu Buhari ne Ministan Harkokin Mai, shi kuma Ibe Kachikwu Karamin Minista. Yayin da Marigayi Maikanti Baru ne Shugaban NNPC a lokacin.

Dan Majalisa Makki ya buga misali da kuma hujja da rahoton NNPC na 2019, wanda ya tabbatar da cewa wadancan gangunan danyen mai har milyan 5.2 babu adadin bayanin su cikin rekod din cinikin mai na shekarar 2018.

Daga nan sai ya bada shawarar a binciki yadda aka rika sayar da danyen mai daga 2018 har zuwa yau.

Matatun man Kaduna, Warri da Fatakwal dai sun dade a mace bas u aiki, amma kuma kullum sai shiga zargin harkalla su ke yi.

Share.

game da Author