Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ita babu ruwan ta da jam’iyyu 74 da soke, jam’iyyun siyasa 18 kadai ta sani kuma su ne za ta yi aiki da su har sai Kotun Koli ta gama yanke hukunci kan jam’iyyun da aka soke rajistar su.
Babban Kwamishina kuma shugaban Kwamitin Wayar da kan Masu Zabe da Yada Labarai na hukumar, Mista
Festus Okoye, shi ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
A sanarwar, ya yi kira ga jam’iyyu 74 wadanda hukumar ta soke rajistar su da su jira hukuncin na Kotun Koli.
Okoye ya ce, “Hukumar Zabe Mai Zaman kan ta ta Kasa (INEC) ta na Kara bada shawara ga jam’iyyun siyasa guda 74 da aka soke rajistar su da su jira hukuncin Kotun Koli kan daukaka Karar da su ka yi game da hurumin Hukumar na soke jam’iyyun siyasa kamar yadda sashe na 225A na kundin Tsarin Mulki ya tanada.
“A shirye Hukumar ta ke a ko taushe ta bi umurnin kotu kuma za ta yi aiki da kowane irin hukunci da Kotun Kolin ta zartar.
“Wannan sanarwar ta zama wajibi saboda ganin yadda wasu daga cikin jam’iyyun da aka soke rajistar su su ke ta turo wa Hukumar Zabe da wasiKu a cikin ‘yan kwanakin nan, su na bayyana niyyar su ta gudanar da zaben share fage tare da kawo sunaye da bayanan ‘yan takarar su a zaben gwamnan Jihar Anambra.
“Jam’iyyun da aka soke din su na kafa bukatar su ta fitar da ‘yan takara a kan hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta bayar a ranar 11 ga Yuni, 11, 2020.
“Hukumar za ta ci gaba da amincewa tare da yin hulda da jam’iyyun siyasa guda 18 kadai masu rajista har sai mun ga yadda aka KarKare batun daukaka Kara daban-daban da ke gaban Kotun Koli.”
Ya Kara da cewa, “Saboda haka, INEC ba za ta sa ido kan kowane irin zaben share fage da kowace daga cikin jam’iyyun da aka soke rajistar su za su gudanar ba kuma ba za ta bayar da kalaman sirri ko karbar suna da bayanan kowane dan takara da aka fitar daga wadannan zabubbukan share fagen.
“Jam’iyyar National Unity Party ta daukaka Kara a kan wannan hukuncin zuwa Kotun Koli ta Nijeriya kuma yanzu haka maganar ta na gaban kotun. Wannan daukaka Karar da wanda Hukumar ta shigar a kan hukuncin Kotun Daukaka Kara da ya danganci jam’iyyu 22 da aka soke rajistar su duk su na gaban Kotun Koli.”
Okoye ya tuno da “cewa a ranar 10 ga Agusta, 2020 Hukumar ta fitar da bayani inda ta nanata cewa hukuncin da Kotun Daukaka Kara ta yanke inda aka ba jam’iyyu 22 da aka soke gaskiya ya saba wa hukuncin da ita dai wannan kotun ta bayar a kan Karar jam’iyyar National Unity Party (NUP) da INEC inda kotun ta tabbatar da ikon hukumar na soke rajistar NUP da sauran jam’iyyun siyasar.
“Bayan ta dubi sabanin da ke akwai tsakanin wadannan hukunce-hukunce biyu, hukumar ta bada shawarar cewa ‘Abin da ya fi alfanu ga tsarin gudanar da zabe shi ne a gama da maganganun biyu a lokaci guda. Tsarin gudanar da zabe zai fi inganta ta hanyar samun matsayar Karshe a kan batutuwan soke rajistar jam’iyyun siyasa da aka yi. Kuma hakan zai bada dama ga hukumar ta tsaya a kan tsandauri maimakon ta je ta na tunanin wane mataki ne cikin da su ke karo da juna za ta yi wa biyayya.”
Ya ce, “A yanzu dai, ana tunatar da jam’iyyu masu rajista da su tabbatar sun kiyaye tanadin da tsarin mulkin su ya tanadar wajen zaben ‘yan takara musamman wajen gudanarwa da fito da ‘yan takara. Wannan ya zama tilas idan aka yi la’akari da dimbin koke-koken da ke biyo bayan rushe Kwamitin Zartaswa na rassan jihohi inda wa’adin su bai Kare ba da kuma umurnin kotu daban-daban masu karo da juna wadanda su ka shafi zaben share fage tsawon lokaci bayan Hukumar Zabe ta gama zabubbuka.
“Girmama Tsarin Mulki da bin doka da oda su ne ginshiKan dimokiradiyya. Don haka ana tunatar da jam’iyyun siyasa irin nauyin da ya rataya a wuyan su na tabbatar da sun bi tsarin dimokiradiyya a cikin gida tare da bin doka da oda.
Discussion about this post