Ba za mu tilasta wa mutane dole sai sun yi allurar rigakafin Korona ba – Minista Mamora

0

Karamin ministan lafiya Olorunnibe Mamora ya bayyana cewa gwamnati baza ta tilasta wa ‘yan Najeriya dole sai sun yi allurar rigakafi ba.

Momora ya ce gwamnati za ta ci gaba da lallaba mutane ne da yi musu karin haske game da alfanun dake tattare da yin rigakafin Korona din.

Da yake amsa tambayoyi daga manema labarai ministan ya ce jihar Kogi bata karbi maganin rigakafin korona ba saboda rashin samar da wurin ajiyan maganin da gwamnatin jihar bata yi ba sannan da rashin samar da ma’aikatan da za su yi wa mutane rigakafin a jihar.

Mamora ya ce akwai yiwuwar cewa siyasa ce ta sa wasu kasashen duniya suka dakatar da amfani da maganin rigakafin AstraZeneca.

Ya tabbatar cewa maganin rigakafin AstraZeneca na da inganci sannan hukumar EMA da WHO sun tabbatar da ingancin maganin.

Bayan haka Mamora ya ce gwamnati har yanzu bata amince wa wani kamfani ya rika shigowa da maganin rigakafin kasar nan ba.

Mamora ya ce hakan zai sa a kaurace wa shigo dsa jabun maganin a Kasar nan.

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta yi kakkausan gargadi ga ’yan Najeriya cewa kowa ya tabbatar ba a dirka masa allurar rigakafin AstraZeneca ta jabu ba.

NAFDAC ta ce kowa ya tabbatar cewa kafin a dankara masa allurar, to ya kasance ita kwalbar ta na dauke da takardar tambarin kamfani sahihiya, kuma gangariya, ba jabun takarda ana manna wa kwalbar ba.

Hukumar ta ce yin wannan kakkausan gargadi ya zama wajibi ga jama’a domin a tabbatar cewa babu wanda aka dirka wa AstraZeneca ta jabu.

Wannan gargadi na cikin wata takardar da NAFDAC ta fitar ga manema labarai, mai dauke da sa hannun Shugabar Hukumar, Mojisola Adeyeye.

An fitar da sanarwar a ranar Lahadi, a Abuja.

Adeyeye ta kara da cewa allurar rigakafin AstraZeneca ta ainihi, ita ce wadda aka kirkiro a Jami’ar Oxford, wato (AZOU), kuma masana’antar hada magunguna ta Indiya, Serum Institute of India (SIIPL) ce ke samar da allurar rigakafin.

Adeyeye ta kara da cewa wannan cibiya ta Indiya ita ce cibiyar samar da allurar rigakafi mafi girma a duniya.

Share.

game da Author