A wani martani da Gwamna Okezie Ikpeazu na Jihar Abia ya mayar wa Sanata Smart Adeyemi a fili, a karon farko, gwamnan ya bayyana cewa kwata-kwata shi ba ya shan giya, kuma ba ya tu’ammali da ita.
“Zan so a ba ni dama na bayyana cewa ni ba na shan giya kwata-kwata, amma kuma ba na kyamar mai shan giya.”
Haka Ikpeazu ya furta a lokacin da ya ke jawabi wurin taron kaddamar da littafin rayuwar Sanata Eyinnaya Abaribe, dan PDP mai wakiltar jihar Abia.
PREMIUM TIMES ta buga labarin dambawar cacar-baki tsakanin hadiman gwamnan Abia da Smart Adeyemi, wanda ya kira gwamnatin jihar Abia gwamnatin ‘yan giya.
Adeyemi kuma ya ce gwamnan dan giya ne.
“Ko a kasashen da ba su da manyan matsalolin da ke damun su kamar mu, shugabannin su na maida hankali ne wajen tattauna batutuwan da su ka shafi tsaro, tattalin arziki da bunkasa rayuwar jama’a. Amma ba su tattauna abin da mutane ke aikatawa ko wanda ba su aikatawa.” Inji Gwamnan Abia.
“A matsayin mu na shugabanni, idan aka dora mana shugabanci, to ya dace murika yin dabi’u da halaye na kwarai wadanda matasa ‘yan baya za su yi koyi da mu nan gaba.
Kafin wannan karin haske na Gwamna Ikpeazu, sai da Gwamnatin Jihar ta bakin Kwamishinan Yada Labaran ta, ya bayyana cewa Sanata Adeyemi fa ‘dan iskan kauye’ ne kawai.
Gwamnatin Nijar Abia ta kira Sanata Smart Adeyemi da cewa ‘dan iskan kauye ne kawai’, wanda ba shi da tarbiyya.
Gwamnatin ta ce ba don Adeyemi na da rigar kariya ta Majalisar Dattawa ba, to da gwamnatin ta Abia ta maka shi kotu, domin a wanke masa idanu daga giribtun kauyancin sa.
Kiran Adeyemi da wannan suna ya biyo bayan shi Adeyemi ya fassara Gwamnan Jihar Abia Ikpeazu cewa tantirin dan giya ne, kuma gwamnatin sa gwamnatin ‘yan giya ce kawai.
Cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai na Jihar Abia, John Okiyi ya fitar ga manema labarai, ya bayyana Sanata Smart Adeyemi da cewa “dan iskan kauye ne, wanda duk a lokacin da ya buda bakin sa, to kalaman sa wawanci ne, sai kuma kara tabbatar da gidadancin sa.
A Je A Yi Gwaji A Gano Mashayin Giya Tsakanin Sanata Adeyemi da Gwamnan Abia –Kwamishina
“Ya kamata Adeyemi ya sani cewa Gwamna Okezie Ikpeazu ba ya daga kwalabe, ba ya shan kowace irin barasa. Kuma ina kalubalantar Sanata Adeyemi ya gayyaci gwamnan Abia su je wani kebantaccen wuri, duk a yi masu gwajin wanda ke da ruwan barasa a jikin sa a tsakanin su, domin a tantance dan giya.
“Kuma idan za a yi gwajin, to Sanata Adeyemi ya je shi da Gwamnan jihar san a Kogi, shi ma a yi masa gwajin, domina tantance wane gwamna ne dan giya, tsakanin na Abia da na Kogi.
“Wai in banda rashin kunya, mutum kamar Sanata Adeyemi, wanda ‘yan jarida ‘yan uwan sa su ka ce shi ne tantagaryar mutumin banzan da ya taba shugabantar Kungiyar ’Yan Jarida ta Kasa, shi ne wai zai kira mutum mai mutunci, Gwamnan Abia wai dan giya.
Discussion about this post