Ba na neman mijin aure wurjanjan kamar yadda ake yadawa a shafukan yanar gizo – Rahama Sadau

0

A daidai jaruma Rahama Sadau na kokarin fahimtar da mutane kan wani labarin karya da wata jarida ta buga cewa wai tana nema miji wurjanjan, sai wasu masu bin ta a shafin Facebook suka fara dankara mata ashar.

Jaruma Rahama Sadau ta gaza hakuri, nan ta ke ta banka masu zagi domin rama abinda suke ce mata.

Daga nan kuma sai aka rabu gida biyu, wasu na tofin Allah Tsine, wasu kuma na yin kira ga jarumar ta yi watsi da irin waɗannan mutane ta daina amsa su.

Mutane akalla sama da Dubu sun tofa albarkacin bakin su kan wannan cece kuce da ya barke tsakanin mabiyan Rahama Sadau da ita da kuma wannan jarida da ta wallafa labarin karya kan jarumar.

A karshe ma cecekucen sai ya koma a tsakanin masu mara mata baya da wadanda ke sukan ta.

Rahama dai ba bakuwa bace wajen fafatawa da mabiyan ta a shafukan yanar gizo.

Jaruma ce da sha yanzu magani yanzu.

A kwanakin baya ta faɗa hauragiya irin haka wanda wani hoto nata da ta saka a shafin Tiwita ya tada jijiyoyin wuya kasarnan inda har sai da manyan malamai da gwamnati duka shiga cikin maganar.

Rahama ta karyata wannan rahotoa na jaridar da ya rubuta wai tana neman miji wurjanjan.

Share.

game da Author