Korafi: Kafofin sada zumunta na yanar gizo sun yi ta yayada hotunan da ke cewa mawakin Amurka, Kanye West ne yafi tarin dukiya cikin bakaken fata ‘yan asalin Kasar.
Hotona da dama aka rika yadawa a kafofin sada zumunta a yanar gizo na kasar Saliyo (Sierra Leone) da wasu kasashe, kan cewa Kanye Omari West shi ne yafi tarin arziki cikin bakaken fatan Amurka, inda ake hasashen cewa karfin arzikinsa ya kai bilyan shidda na dalar Amurka.
Kafofi da yawa sun wallafa wannan labarin a cikinsu har da kafar labaran nishadi na Complex wadda ta ce darajar kamfanin takalman West mai suna Yeezy da na kayan sawa wanda kamfanin Gap ta kulla yarjejeniya da shi, sun kai Biliyan 4.7 na dallar Amurka.
Wannan labari ya yadu a shafukan WhatsApp da Instagram ba tare da an bayar da wani bayani mai gamsarwa ba.
Wannan labari na Kanye West dai ya yi mafari ne bayan da tashar hada-hadar kasuwanni na Bloomberg ta wallafa labari mai cewa kamfanin GAP na da burin samun biliyoyin dala daga yarjejeniyarta da Kanye West.
Tantancewa
Bai zama wani abin boyewa ba cewa mawaki Kanye West ya samu makudan kudi bayan da ya shawo kan rikicin basussukan shi, ya kuma kulla yarjejeniyar takalman Sneaker mai suna YEEZY da kamfanin takalma na Adidas. Jaridar FORBES tana kiyasin darajar yarjejeniya zai kai dalar Amurka biliyan 1.7.
To sai dai idan har aka hada kudin da ya samu daga takalman Yeezy, da kudin da ya ajiye a banki, da kadarorin sa, da abun da yake samu daga wakoki da ma Skims – kamfanin rigunan matan da hadin gwiwa ne da matarsa Kim Kardashian, gaba daya Kudin bai kai dala biliyan shidda ba.
Jaridar Forbes ta bayar da bayani kan kudaden Kanye West kamar haka:
Yeezy: Dala biliyan daya da rabi ($1.5 billion)
Kudi mafi yawa a dukiyar West, ya samu ne daga yarjejeniyar dake tsakanin sa da kamfanin takalma na Adidas. A bara kudin ya karu zuwa dala biliyan 1.7 daga dala biliyan 1.3 a shekarar 2019. Anan ne ya samu karin arziki har dala milliyan 191 daga ribar da siyar da takalman suka yi.
Duk da cewa UBS na hasashen cewa takalman za su kai wajen dala biliyan uku a shekara ta 2026 mu mun yi amfani da adadin kudin da ke kasa ne a shekara ta 2020.
Kudi da Kaddarori: Dala Miliyan 160 na Amurka
Sakamakon masu sauraron wakokin da Kanye West ya yi a faifan da ya kira Yeezy, mawakin ya sami kudi sosai hade da gidaje da kayayyakin wasar yara. A gidaje kawai, yana da wadanda suka kai darajar dala milliyan 100 na Amurka wadanda suka hada da filayen kiwo da na noman da ya mallaka a jihar Wyoming da kuma yankin Los Angeles.
Bisa bayanan wasu takardun bankin da ma’aikatansa suka aiko mana, yana da zanannun hotunan da ke da darajar dala milliyan tara, da kayan ado irin na zinari da lu’u-lu’u, su kuma sama da miliyan bakwai na dala, sannan motocin dala miliyan biyar, kayan kujeru na dala miliyan uku da ‘yan kai sai kuma dabbobi na dala miliyan daya.
Bayan haka, yana da bashin da ya kai miliyan 56 na dala.
Wakoki: Dala miliyan 90.
Duk da cewa mafi yawan arzikin Kanye West a yanzu haka daga fanin kawa da kwalisa ne, ya fara samun kudi ne daga kidan rap inda ya kasance daya daga cikin fitattu a wannan salon wakar, kuma yawancin wakokin na cigaba da kawo mi shi kudi kowace shekara kamar yadda yake samu daga faifan Yeezy yanzu. Zai iya ma cin bashi ya biya da kudaden wakokin da basu riga sun shigo hannu ba, kamar yadda mayan mawaka irin su Shakira da Bob Dylan suka yi a bara.
Kamfanin Skims: Dala miliyan 64
West da matarsa Kim Kardashian West wadda ke shirin rabuwa da shi nan ba da dadewa ba, suke da kamfanin skims wadanda ke dinka kayayyakin mata. Kuma kamfanin ya kara fadada a lokacin annobar COVID-19.
Wannan labari da aka samu na dala biliyan shida, kiyasin da shafin hada-hadar kasuwanni na Bloomberg ta yi ne, inda ta hada jimilar kudin da mawakin ke da su yanzu da hasashen kudin da zai samu nan gaba a wasu yarjeniyoyi da yayi da kamfanonin da ke saida kayan sawar sa nan gaba.
Wannan yarjejeniya na iya ninka arzikin mawakin amma ba ta riga ta fara aiki ba domin ba’a fara sayar da kayayyakin ba. Shi ya sa jaridar Forbes bata ba da wani kiyasi ba, tana jira har sai sadda aka fara sayar da rigunan aka ga irin cinikin da aka yi.
A wani bayanin da ta yi jaridar Forbes ta ce:
“Rahoton cewa arzikin mawakin ya kusan dala biliyan bakwai ba haka bace, tunda ba a yi cinikin wasu kayayyakin ba tukuna. Shi ya sa a yanzu haka karfin arzikin sa ya tsaya a kan kashi daya cikin ukun wannan adadin da ake bayyanawa.”
Rahoton UBS din da Bloomberg ke danganta labarinta da shi, hasashe ne kawai.
A Karshe
Yadda zargin cewa Kanye West shi ne ya fi tarin dukiya a tsakanin bakaken fata ‘yan asalin Kasar Amurka ya rika yaduwa a kafofin sadarwar Saliyo ya sa DUBAWA ta gudanar da wannan bincike domin domin tsage gaskiyar karfin arzikin mawaki Kanye West.
Forbes ta ruwaito cewa bakin fatan da yaki kowa karfi arziki da tarin ukiya a Amurka shi ne Robert F Smith mai kamfanin Vista Equity wanda ke da tarin dukiya da ya kai biliyan shida na dalar Amurka. Saboda haka, DUBAWA tana tabbatar da cewa Kanye West bai kai wannan matsayi ba tukuna.