Sanata Dino Melaye ya ce yaudarar da aka yi sannan aka yi masa rufa-rufa ya rika tallata Buhari a 2015, ashe-ashe abin duk yaudara ce.
Dino ya ce idon sa sun rufe ne a lokacin da aka rika ruɗar sa da wasu su bi Buhari, amma kuma da idon sa suka bude nan ne ya gane ashe ajandar Buhariyya , ajandar Buhariyya yaudara ce kawai.
Waɗannan sune irin kalaman da Dino ya yi a lokacin da yake hira da talbijin din Channels ranar Juma’a.
” Yadda kasan siddabaru da rufa ido haka aka yi mana muka yi na’am da Buhariyya, ashe kafcecen yaudara ce kawai, muka yi a lokaci. Gashi mun kwan ciki. Wannan shine dalilin da ya sa wasun mu muka tattara muka fice daga jam’iyyar APC domin mun gano cewa duk abin yaudara ce.
Dino ya kara da cewa jam’iyyar APC ta zama kungiya ba jam’iyya ba.
” Tabbas APC kungiya ce yanzu ba jam’iyya ba. Domin duk jam’iyyar da bata da shugaba, bata wadanda suke gudanar da ayyukanta kamar yadda doka ta gundaya, ta zama kungiya.
” Duk matsalolin da muke ciki a PDP yanzu ‘kungiyar’ APC ce ku yi mana zagin kasa.
Da aka tambaye shi ko matsayar kwamitin jam’iyyar na a bari kowa ya fito takarar shugaban kasa a PDP maimakon karba-karba da aka san jam’iyyar da shi, Dino ya ce har yanzu ba a yi zama ta musamman ba gane da wannan rahoto na kwamitin.
” Idan jam’iyya ta zauna za a tattauna daga nan za a samu matsaya daya akai. Amma yanzu bani da abinda zan ce har sai jam’iyya ta zauna ta duba kwamitin.
“APC fa yanzu ba jam’iyya ba ce, Kungiya ce kawai, saboda tsananin rudewa da jam’iyyar ta yi da rarrabuwar kai. Na daya akwai bangaren El-Rufai da Amaechi, sannan akwai bangaren Tinubu da tawagarsa sai kuma bangaren Fayemi da Fashola suma na su da ban.”