Kamfanin mai na kasa ya musanta karin kudin mai da hukumar PPPRA ta sanar ranar Alhamis.
Idan ba a manta ba PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito cewa Hukumar dake tsarawa da kyayyade farashin man fetur PPPMC ta bayyana cewa za a rika siyar da lita ɗayan man fetur a gidajen mai naira N209.61 da N212.61 daga ranar Juma’a.
Wannan sanarwa da hukumar ta fitar a yammacin Alhamis ya girgiza ƴan Najeriya ganin da kanta kamfanin mai ta Kasa ta karyata cewa wai gwamnati zata kara kuɗin mai tun a farkon wannan wata na Maris.
Shugaban kamfanin mai na kasa Mele Kyari ta hannun shugaban sashen hulda da jama’a, Kennie Obateru, ya bayyana cewa kamfanin man ba za ta kara kudin mai ba kamar yadda ake ta yadawa a wancan lokacin.
A lokacin har da yin kurin cewa ba za ta yi haka ba saboda kada Talakawa su tagayyara ne.
Kowa dai ya san abinda zai biyo baya akan kayan masarufi da kudin shiga motocin haya.
Tun a makon jiya gidajen mai a fadin kasar na suka daina sai da mai a dalilin shirin kara farashin litar mai layukan motoci suka fara bayyana a gidajen mai, a hankali cikin kwanaki biyu sai wahalar mai ya yi tsanani musamman a jihar Legas da babban birnin tarayyar, Abuja.
Sai dai kuma, a ranar juma’a kamfanin ta karyata karin kudin man. Kamfanin ya ce ba za a kara kudin mani ba.
Haka ita ma hukumar PPPRA ta cire sanarwar karin kudin man wanda ta saka a shafinta ta tiwita.