ASTRAZENECA: Hukumar NAFDAC ta ce ’yan Najeriya su yi kaffa-kaffa da rigakafin jabu

0

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta yi kakkausan gargadi ga ’yan Najeriya cewa kowa ya tabbatar ba a dirka masa allurar rigakafin AstraZeneca ta jabu ba.

NAFDAC ta ce kowa ya tabbatar cewa kafin a dankara masa allurar, to ya kasance ita kwalbar ta na dauke da takardar tambarin kamfani sahihiya, kuma gangariya, ba jabun takarda ana manna wa kwalbar ba.

Hukumar ta ce yin wannan kakkausan gargadi ya zama wajibi ga jama’a domin a tabbatar cewa babu wanda aka dirka wa AstraZeneca ta jabu.

Wannan gargadi na cikin wata takardar da NAFDAC ta fitar ga manema labarai, mai dauke da sa hannun Shugabar Hukumar, Mojisola Adeyeye.

An fitar da sanarwar a ranar Lahadi, a Abuja.

Adeyeye ta kara da cewa allurar rigakafin AstraZeneca ta ainihi, ita ce wadda aka kirkiro a Jami’ar Oxford, wato (AZOU), kuma masana’antar hada magunguna ta Indiya, Serum Institute of India (SIIPL) ce ke samar da allurar rigakafin.

Adeyeye ta kara da cewa wannan cibiya ta Indiya ita ce cibiyar samar da allurar rigakafi mafi girma a duniya.

“AZOU ta bai wa cibiyar SIIPL lasisi da lakanin samar da ruwan allurar AstraZeneca mai tarin yawa domin sayarwa a dunya. Kuma sai da su ka rattaba hannun yarjejeniya tukunna.

“Daga nan ne ita kuma Cibiyar Hada Magunguna ta SIIPL ta rada wa ruwan allurar rigakafin suna COVISHIELD, bayan cimma yarjejeniyar amincewa daga Jami’ar Oxford. Wato COVISHIELD da AstraZeneca duk daya ne.

“SIIPL babbar cibiyar hada magungunan rigakafi ce. A can ne ma aka samar da rigakafin cututtuka da dama, ciki har da kyanda, tetanus da shan-Inna (polio).

A karshe ta ce wannan rigakafi Majalisar Dinkin Duniya ta amince da ita, kuma kasashe kimanin 170 na amfani da ita.

Share.

game da Author