Jam’iyyar APC ta kafa kwamitin mutum takwas wadanda aka dora wa alhakin sake nazarin dokokin ta kafin zaben 2023 mai zuwa nan da shekaru biyu.
Babban Sakataren Riko na APC, John Akpanudoedehe ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke kaddamar da kwamitin Sake Faslin Dokokin APC, a ranar Talata, a Abuja.
“A matsayin APC na jam’iyyar jama’a, karkashin shugabancin Gwamna Mai Mala Buni, ta yi amanna cewa idan ana batun sake gina jam’iyya, to tilas a sake dubawa domin a shimfida muradun da za su faranta wa masu jam’iyyar rai, wato talakawan kasar nan.” Inji shi.
“Akwai bukatar sauya wasu dokikin jam’iyya, sabo jam’iyyar a yanzu ta karu, ta bunkasa kuma ta fadada, har ta zama a Afrika babu wata jam’iyyar da ta kai ta yawn mambobi a fadin Afrika.
“Bisa wannan dalili ne ya zama wajibi mu sa dokokin da za su kasance mafi sahihanci a kasar nan a jam’iyyance.”
Ya kara da cewa jam’iyyar APC ta roki kwamitin a matsayin sa na kasa baki daya, ya roki duk da a bijiro da wasu sabbin ka’idojin da za su amfani kasar nan baki baya da jam’iyyar APC tare da magoya bayan su baki daya.
Tahir Mamman ne Shugaban Kwamitin Sake Nazarin Dokokin Kundin tsarin mulki. Shi kuma jan-hankali ya ci cewa ya na neman shawarwari daga masu ruwa da tsakin APC.
Sauran mambobin kwamitin sun haa da Dakas Dakas, Akinremi Olaide, Ego Ezuma, Mohammed Kumaila, Shuaibu Aruwa and Ekokoi Solomon.
Wannan ne karo na biyu da APC ta sake nazarin kunin dokokin jam’iyyar, tun daga kafuwar jam’iyyar a cikin 2013.