Wata gobarar da ta fara ci a Kasuwar Sabo da ke garin Oyo na Jihar Oyo misalin karfe 10 na dare, ta yi wa kasuwar kurmus.
An ce bayan wutar ta tashi wajen 10 na safe, sai ta rika mamaye kusan dukkan sauran sassan kasuwar.
Lamarin ya faru ne daidai lokacin da masu safarar kayan abinci da dabbobi su ka kaurace wa kasuwannin kudancin kasar nan.
Sun ce sun kaurace ne saboda kisa da kone masu dukiya da ake yi ba tare da biyan su diyya ba.
Wannan kauracewa da kayan abinci daga Arewa, ta haifar da matsananciyar tsadar abinci a kusan dukkan sassan kudancin kasar nan.
PREMIUM TIMES ta ji daga majiya mai tushe wadda ta ga irin ta’adin da gobarar ta yi cewa an yi asarar kaya na bilyoyin nairori.
Wasu ‘yan kasuwar da su ka yi asarar makudan kudade da dukiyoyi na ta jimamin wannan bala’i da ya auka masu.
Sai dai kuma har yau ba a san dalilin tashin wannan gobara ba, wadda ta ce kasuwar da akasarin masu kantinan cikin ta duk Yarabawa ne, ba kamar kasuwar Shasha da Hausawa su ka yi wa kaka-gida ba.
Yayin da masu kashe gobara su ka garzaya cikinndaren sun a aikin kokarin kashe gobara, PREMIUM TIMES ta kasa jin ta bakin Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Oyo, Adeleke Ismail da kuma Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sandan Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi.