Ana ci gaba da samun karancin wadanda suka kamu da Korona a Najeriya, mutum 600 kacal suka kamu cikin kwananki 7da suka wuce

0

Daga ranar Lahadi zuwa Alhamis na wannan mako mutum 624 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya sannan mutum 6 sun mutu.

Bisa ga wannan sakamako da hukumar NCDC ta fita ya nuna yadda cutar ke kara yi wa Najeriya bankwana.

Idan ba a manta ba a makon da ya gabata mutum 869 suka kamu da cutar sannan mutum 11 suka mutu a kasar nan.

A wannan mako mutane sun fi kamuwa da cutar a ranar 23 ga watan Maris inda a wannan rana mutum 214 ne Suka kamu.

Sannan a ranar 25 ga Maris an fi samun yawan mutanen da cutar ta yi ajalinsu inda mutum biyar ne suka mutu.

Zuwa yanzu an yi wa mutum 1,727,467 gwajin cutar inda daga ciki mutum 162,275 Suka kamu.
An sallami mutum 149,882 sannan mutum 2,036 sun mutu.

Har yanzu mutum 10,357 na killace a asibitocin kula da masu fama da cutar a kasar nan.
Najeriya ta yi wa mutum 122,410 allurar rigakafin korona, samfurin AstraZeneca.

Shugaban hukumar kiwon lafiya a matakin farko (NPHCDA), Faisal Shu’aib ya ce har yanzu babu wani rahoton samun matsala ko da daya ne a kasar nan da aka fara yi wa mutane rigakafin korona.

Ya yi kira ga yan Najeriya musamman masu fama da wasu cututtuka banda Korona da su garzaya wuraren da ake yin rigakafin Korona ayi musu.
An kawo akalla kwalaben rigakafin AstraZeneca guda milyan 4 a Najeriya.

Shugaban kwamitin PTF Boss Mustapha ya ce kamfanin MTN ta kawo wa Najeriya kwalaban maganin rigakafin cutar 300,000 ranar Lahadin da ya gabata.

Sai dai kuma yayin da ake ci gaba da yin allurar ta AstraZeneca a Najeriya, wasu kasashe da su ka hada da Jamus, Italy, Faransa, Netherlands, Ireland, Austria, Afrika ta Kudu da sauran kasashe da dama irin sun dakatar da yi wa al’ummar kasashen su rigakafin AstraZeneca, biyo bayan rahotannin cewa allurar na haddasa toshewar magudanan jini a cikin jikin wanda aka yi wa allurar.

Bayan haka Shu’aib ya ce gwamnati ta raba wa duk jihohin kasar nan maganin rigakafin banda jihar Kogi.

Ya ce jihar Kogi bata karbi maganin rigakafin ba saboda rashin samar da wuraren ajiye maganin rigakafin da daukan ma’aikatan da za su yi wa mutane allurar rigakafin.

Share.

game da Author