An yi garkuwa da daliban makarantar firamare da malaman su a Kaduna

0

Da safiyar Litinin ne ‘Yan bindiga suka afka makarantar firamare dake Remi,Karamar Hukumar Birnin Gwari, suka kwashe yaran makaranta da malamai suka nausa daji da su.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar litini.

Aruwan ya ce gwamnati bata gama tantance yawan dalibai da malaman da aka arce da su ba har yanzu.

Sai dai ya ce da zaran an sami adadin yawan wadanda aka sace zai sanar ya duniya.

Wannan shine karo na uku a jere da ake afkawa makarantun Kaduna don ana sace dalibai.

Idan ba a manta ba bayan sace daliban makarantar fasaha da raya gandun daji, wanda har yanzu ba asako akalla dalibai sama da 30 ba, mahara sun afka makarantan kwana a Ikara, sai dai nan ba su yi nasarar sace kowa ba.

Bayan haka sun dira makarantar kimiya dake Ikara, amma anan ba su yi nasarar tafiya da ko mutum daya ba.

Maharan da suka sace daliban makarantar Forestry, na Kaduna sun bukaci a biya su kudin fansa har naira miliyan 500 kafin su sako daliban.

Share.

game da Author