Dimbin matsalolin rashin tsaron da su ka mamaye kasar nan, ba su hana Ministan Harkokin Tsaro Bashir Magashi furta cewa an samu zaman lafiya a Najeriya ba.
Minista Magashi ya kara da cewa goyon bayan da Majalisar Dattawa da ta Tarayya ke bayarwa ga Ma’aikatar Tsaro zai ci gaba da yin tasiri wajen samar da zaman lafiya mai dorewa a kasar nan.
Ya ce “sojojin Najeriya sun samu nasarar dawo da zaman lafiya a yankin Arewa maso Gabas”. Haka dai Magashi ya bayyyana a ranar Talata, cewa “har maa wasu sassan kasar nan, an samu wanzuwar zaman lafiya.”
Ya yi wannan ikirarin ne a lokacin da Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Harkokin Tsaro na Sojoji, Sanata Aliyu Wamakko ya kai ziyarar duba-gari a ofishin Minista Magashi.
Manjo Janar Mai Ritaya Magashi, duk da ya ce Najeriya na ta fama da kalubalen matsalolin tsaro a cikin gida, ya yi tsinkayen cewa an samu dawo da zaman lafiya a wasu sassan kasar nan, inda masu garkuwa da mutane su ka rika kai hare-hare a baya.
“Najeriya na fama da matsalolin tsaro daban-daban, inda Boko Haram da ’yan bindiga ke ci gaba da amfani da muggan makamai a jihohin Neja, Katsina, Kaduna, Sokoto da Zamfara.”
“Sojojin Najeriya na ci gaba da dakile wannan barazana ta gabagadi a sassan kasar nan, musamman a Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
“Wadannan kalubale sun haifar da asarar rayukan zaratan sojojin Najeriya masu tsantsar kishin kasa da su ka sadaukar da rayuwar su ga kasar nan.
“Amma kuma duk da wannan kalubale, sojojin Najeriya sun samu nasarar wanzar da zaman lafiya a wasu sassan kasar nan.” Inji Magashi.
Idan ba a manta ba, PREMIUM TIMES HAUSA ta ruwaito Babban Hafsan Askarawan Najeriya na cewa sojoji za su kwankwatsi duk wata barazanar da ake wa tsaro a Najeriya.
Sojojin Najeriya za su kwankwatse duk wata barazanar da matsalar tsaro ke wa kasar nan –Janar Attahiru.
Discussion about this post