An kama dan sandan da ya saci bindigogi AK-47 guda biyar

0

Wani dan sandan Mobal mai suna Shedrack Igwe ya shiga hannun jami’an tsaro, bayan sata a rumbun ajiyar bindigogin Mobal na Shiyya ta 28 da ke Umuahia shiga a jihar Abia, ta bindigogi biyar samfurin AK-47.

An tabbatar da cewa Igwe wanda kurtun dan sandan Mobal ne da ke tsaron rumbun najiyar makaman, ya samu yin satar tare da taimakon wasu.

Sai dai kuma bai yi nasarar tserewa ba, domin an yi cacukui da shi a cikin Karamar Hukumar Ikwo ta Ebonyi, inda can din ne mahaifar sa.

Ya dankara satar bindigogin a ranar 2 Ga Maris, wadda dalilin haka ne ya tsere zuwa Ebonyi din, amma aka bi shi har can aka damke shi.

Yanzu dai ya na hannun jami’an tsaron Abia, bayan da jami’an tsaron Bayelsa. Kuma ana ci gaba da binciken sa.

Bindigogin guda biyar samfurin AK-47 kuma da ya sace, duk an same shi tare da su a kauyen su.

Ana tunanin kuma tabbas ya sha dauka a baya ya na sayarwa, amma dai har lokacin rubuta wannan labarin, ba a kammala tabbatar da ko guda nawa ya taba sunguma ya sayar a bayaba, kafin a kama shi da wadannan guda biyar din.

Ana ji ma wasu Keke-Napep guda uku da ya saya kwanan baya, da kudin cinikin wasu bindigogin ya saye su. Saboda dai kurtun dan sanda ne, ba wata sana’a gare shi ba.

Bayan ya sayi Keke-Napep guda uku, ya damka su ga wani dan uwan sa mai suna Ifeanyi Igwe.

Wani jami’in yan sanda a Ebnyi ya bayyana cewa, “Wannan abin kunyar satar bindigogi da dan sanda ya yi a Ebonyi, ya nuna rashin iya aiki da kuma wasareren da aka yi da makamai accikin rundunar ‘yan sanda. Daukar kurtun dan sanda a damka masa aikin tsaron makamai, babban kuskure ne.”

“Kuma abin mamaki aka dauki wannan muhimmin aiki aka damka masa, ba tare da auna halayen sa ba, kuma ba tare da rika sa-ido a kan sa ba”.

An tuntubi Kakakin Yada Labarai na ‘Yan Sanan Abia, Geofrey Ogbonna, ya shaida cewa ba ya kusa.

Share.

game da Author