Babbar Kotun Jihar Legas da ke Ikeja ta daure Raymomd Akanolu shekaru bakwai a gidan kurkuku, saboda badakalar karkatar da dala 32,000 lokacin da ya ke aiki a matsayin Babban Manajan Dangote Industries Limited.
Cikin wata sanarwa da Kakakin Yada Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya fitar a ranar Talata, ya ce an daure Akanolu shekaru bakwai tare da Mojisola Aladejobi da kuma wani mai suna Balogun Alaba.
An dai gurfanar da su ukun ne a gaban Mai Shari’a S.S. Ogunsanya, inda aka tuhume su da aikata laifuka biyu da su ka hada da kokarin satar kudin da ba hakkin su ba har dala 32,000.
Tun da farko dai sun bayyana cewa ba su aikata laifin ba, wanda haka ya sa kotu ta fara shari’a gadan-gadan domin tabbatar da sun aikata ko ba su aikata ba, kamar yadda su ka ce ba su aikata din ba.
Masu gabatar da kara, S.O. Daji da Babatunde Sonoiki, sun kira masu bayar da shaida, sannan kuma su ka damka wa kotun wasu kwafe-kwafen takardun da ke tabbarar da laifi a kan wadanda ake tuhuma din.
“An same su da laifin kara wa kudin inshorar wani jirgin DIL na kamfanin aringizon kudin inshorA har naira karin dala 32,000 kan jirgin mai lamba No. 52-DGN.”
“Laifin da su ka aikata ya saba wa Doka mai Sashe na 323 na Dokokin Laifuka na Jihar Lagos, mai lamba No. 11 ta shekarar 2011.” Inji EFCC.