AN CI MORIYAR GANGA: Yadda Buhari ya kafa ministoci babu matasan da su ka cicciba shi ya hau kan mulki

0

PREMIUM TIMES ta yi nazarin Minsitocin Buhari su 44, wadanda bincike ya nuna cewa akasarin su ’yan shekaru 61 ne abin da ya yi sama.

Wani abu da zai kara zama bambarakwai a ckin ministocin, shi ne Ministan Matasa, Sunday Dare, ba matashi ba ne, dattijo ne mai shekaru 54. Wato an haife shi a shekarar da aka kashe su Sardauna da Tafawa Balewa.

Cikin 2003, shugaban lokacin Olusegun Obasanjo ya yi rawar gani, inda ya nada ministoci biyu duk matasa. Su ne Chukwumeka Chikelu mai shekaru 36, sai kuma Frank Nweke mai shekaru 37.

Sai dai kuma shekaru 18 bayan wannan lokacin, an ci gaba da maida matasa sanyar-ware, bayan an ci moriyar su wajen kafa gwamnati tare da su.

Musamman ma Gwamnatn Shugaba Muhammadu Buhari, wadda za a iya cewa wata guguwar sauyin tunanin matasa ne ya kafa gwamnati har ta yi nasara a karkashin tafiyar Buhariyya.

Tsarin Najeriya dai ya bayyana matashi shi ne dan shakara daga 18 zuwa 35, amma a cikin 2009, an sake tsari, inda aka takaita shekaru matasa daga 18-29.

Sai dai har yau Yarjejeniyar Afkrika, ita ta amince ne daga shekaru 18 zuwa 35.

Gurguzun Dattawa A Ministocin Buhari:

Karamin Ministan Harkokin Niger Delta, Tayo Alasoadura, shekarar sa 71; Minstan Harkokin Lafiya, Osagie Ehanire, shekarun sa 74; Ministan Harkokin Noma, Sabo Nanono, shekarun sa 74; Ministan Tsaro Bashir Magashi, dattijo ne dan shekara75; sai kuma Ministan Harkokin Fetur, wanda ya fi kowa tsufa, shi ne Muhammadu Buhari, mai shekaru 78.
‘Matasa’ A Ministocin Buhari:

Minista Sadiya Farouq ta Ma’aikatar Harkokin Jinkai, Agaji da Inganta Rayuwar Marasa Galihu, ita ce mai karancin shekaru 46 a cikin ministocin Buhari.

Sai kuma Minista , Isa Pantami, shekaru 48; Sai Karamar Minstar FCT Abuja, Ramatu Tijjani mai shekaru 50; Ministan Tama da Karafa, Ikechukwu Ogah, shekarun sa 51; sai Karamin Ministan Kwadago, Festus Keyamo, mai shekaru 51.

Ministoci 17 cikin 44 sun tashi daga dattawa masu shekaru 60 zuwa 69.

Wasu 20 kuwa daga masu shekaru 50 zuwa 59.

‘Wa Ke Ta Minista, Matasa Na Neman Ciyamomi Ma An Hana Su!’ –Ismail Garba

Wani matashi ya bayyana wa PREMIUM TIMES Hausa ta wayar tarho cewa ai gwamnatin Najeriya ta bar matasa a tasha, tun bayan da aka yi wa Buhari lodi ya tuka mota ya fice.

“Mun yi zaton za a samu matasa a cikin ministocin Baba, ganin yadda ya rika jan matasa a jika, domin su ne ke tafyar da Guguwar Buhariyya. To amma sai mu ka ga ana ta kwasar dattawa ana lodawa a motar daukar ministoci.

“Kuma har ta kai ga an dora mai shekaru 54 wai ministan matasa, ai magana ta kare, duk matashi ya san an yi ba da shi ba.

“Shin ba mu ne mu ka kafa gwamnatin ba? Lokacin da Baba ke cewa. “mu kasa, mu tsare, mu raka, ai da mu matasa ya ke ba da dattawa ba. Wane dattijo ne zai iya fita gwagwarmayar a kasa a tsare? Sai dai matasa. Amma mun kasa, mun tsare wa dattawa kuri’u, sun hau sun bar matasa na jiran a sake zuwa a ce su kasa su sake tsarewa.

“Ko ciyaman na Karamar Hukuma matashi ya nema, sai ya ga an sa kafa an hambarar da shi.” Inji Garba.

Ya ce idan kuwa ka ga matashi a wani mukami mai tsoka, to ka binciki asalin sa.

Share.

game da Author