Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta dawo Najeriya bayan shafe watanni shida a kasar Dubai tana hutawa.
Rahotanni a baya sun nuna cewa tun bayan bikin ‘Yar ta Hanan, ta tattara nata-inata ta koma can Dubai da zama shi kuma maigida Baba Buhari na Najeriya a duk tsawon watannin nan da bata nan ya na ci gaba da gudanar da mulki.
An rika ruwaitowa cewa dalilin waskewa Dubai da Aisha tayi na da nasaba da rashin zaman lafiya da rudani da take fuskanta a fadar shugaban kasa, wanda ba mu tabbatar da haka ba.
Shi ko Aliyu Abdullahi, wato Kakakinta cewa yayi ba zai iya tabbatar da ko ta dawo ba ko bata dawo ba. Iya abin da zai iya fadi kenan a lokacin da PREMIUM TIMES ta nemi ji daga bakin sa.
Tun bayan bukin Hanan Buhari, Aisha ta yi tsit ba a jin duriyar ta a kasar nan. Ba a taro ba ba kuma a wani sha’ani na gwamnati ba. Hakan yasa mutane na ta tofa albarkacin bakin su game da haka.
Yanzu dai ba a san takameiman abinda ya dawo da ita ba. Ta dawo ne ta ci gaba da zama kamar da ko kuwa ta dan leko ne bayan kwana biyu ta karkada ta koma abinta.